‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a Kamaru

An  zargi ’yan kungiyar Boko Haram da kai hari a  garin Gamboru mai makotaka da Fotokol, d ake kasar Kamaru karshen makon jiya a kusa da a Arewacin kasar, inda harin ya haifar da asarar rayukan jama’a bakwai, cikinsu har da sojan Kamaru guda da wasu fararen hulashida  da ake kyautata zaton cewa suna daga […]

‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a Kamaru
‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a Kamaru

An  zargi ’yan kungiyar Boko Haram da kai hari a  garin Gamboru mai makotaka da Fotokol, d ake kasar Kamaru karshen makon jiya a kusa da a Arewacin kasar, inda harin ya haifar da asarar rayukan jama’a bakwai, cikinsu har da sojan Kamaru guda da wasu fararen hula
shida  da ake kyautata zaton cewa suna daga cikin ayarin kungiyarda ta kai hari.
Hukumomi a Kamaru sun ce mutane biyu  ne kawai suka mutu, wato ke nan mutum guda daga kowane bangare. Bayanai sun nuna cewa sojojin Kamaru ne suka maida martani akan ’yan kungiyar Boko Haram bayan sun kashe musu takwaran aiki.
’Ya’yan kungiyar biyu na hannun ‘yan sandan Kamaru a yankin Arewacin kasar. Shugaban wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “Os-cibile droits de l’homme” ya bayyana wa wani kamfanin dillancin labarai cewa, bayan shigowar ‘yan kungiyar Boko Haram ne ta wata barauniyar hanya, mazaunin wani kauye ya sanar wa ‘yan sanda shigowar wasu mutane dauke da bindigogi da ake kiyasta yawansu akan kusan 30. Bayan sojojin Kamaru  da suke zaune akan iyaka suna aikin tabbatar da tsaro sun cin musu domin sanin masabbabin abinda ya shigo da su Kamaru da kuma manufar da suke dauke da ita ne rigima ta fara kunno kai a tsakaninsu. Bayan ‘yan kungiyar sun gano
cew dakarun Kamaru  na niyyar yi musu kwanton bauna ne , daga nan ne su kuma suka fara yin harbe-harbe. Hakan ya kaiga bangarorin biyu yin musayar harbin a tsakaninsu. A dalilin hakane jami’an tsaro suka  aika Karin wasu sojoji na Bataliyar kai dauki da  gaggawa wadanda ake kiransu “BIR” a taikace domin su rufa wa takwarorinsu baya.
Wata majiya ta ce kuma ‘yan kungiyar Boko Haram sun shigo Kamaru ne, domin neman mafaka bayan sun yi artabu da sojojin Najeriya sakamakon hare-haren makon jiya da aka kai a garuruwan Shuwa da kuma Madagali a Jihar Adamawan Najeriya da kuma wasu kauyuka na Jjihar Borno.
Ministan sadarwa Issa tchiroma Bakary ya yi, ya nuna cewa babu wata yarjejeniya tsakanin Kamaru da Najeriya game da bai wa dakarunta damar shigowa Kamaru, su mayar da martani, ko kuma su kama ’yan kungiyar Boko Haram.