’Yan kungiyar Seleka 17 sun mutu a Afirka ta Tsakiya

Kakakin kungiyar Musulmi ta Seleka, Kyaftin Ahmat Najat ya bayyana cewa mutum 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata arangama tsakanin membobin kungiyar a arewacin  Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ranar Talata.Akwai kuma wasu mutum uku da suka ji raunuka a rikicin da ya barke ranar Litinin a wani yanki da ’yan Selekan ke da rinjaye […]

’Yan kungiyar Seleka 17 sun mutu a Afirka ta Tsakiya
’Yan kungiyar Seleka 17 sun mutu a Afirka ta Tsakiya

Kakakin kungiyar Musulmi ta Seleka, Kyaftin Ahmat Najat ya bayyana cewa mutum 17 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata arangama tsakanin membobin kungiyar a arewacin  Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ranar Talata.
Akwai kuma wasu mutum uku da suka ji raunuka a rikicin da ya barke ranar Litinin a wani yanki da ’yan Selekan ke da rinjaye mai suna Bambari.  Kodayake har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a fahimci dalilin da ya haifar da arangamar ba tukuna.
kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin rikicin siyasa ne tun bayan da kungiyar Seleka, wadda ita ce kungiyar Musulmi ’yan tawaye da hadin gwiwar wasu mayaka da suka fito daga kasar Sudan da Chadi , ta karbe mulkin kasar a watan Maris din bara.
Sakamakon wannan ya sa kungiyar Kiristoci ta anti- Balaka ta dauki makamai a wani mataki na adawa da hakan. Amma ko bayan murabus din gwamnatin karkashin jagorancin Shugaba Michel Djotodia tashin hankalin bai tsaya ba. Tun daga lokacin yawancin Musulmi da ke zaune a kudancin kasar suke kauracewa muhallinsu saboda yadda suke fuskantar farmaki.
Kodayake akwai kimanin  dakaru 2,000 daga kasar Faransa da kuma wasu guda 6,000 daga kungiyar Tarayyar Turai da ke aikin samar da zaman lafiya a can.
A ranar 10 ga watan nan ne shugabar wucingadin kasar, Catherine Samba-Panza ta nada Mahamat Kamoun a matsayin sabon Firaminista. Mista Kamoun, wanda Musulmi ne, ya fuskanci adawa ba wai daga ’yan anti-Balaka ba kawai, amma har daga wasu membobin kungiyar Seleka.