’Yan kwadago sun yi barazanar sake komawa zanga-zanga

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta gaggauta janye karar da ta kai su

’Yan kwadago sun yi barazanar sake komawa zanga-zanga

Joe Ajaero

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi barazanar sake komawa zanga-zanga a ranar 14 ga watan Agusta matukar Gwamnatin Tarayya ba ta janye karar da ta shigar da ita ba.

Kungiyar ta yi gargadin ne bayan taron Majalisar Zartarwarta da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.

A ranar Laraba ce dai Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Shari’a ta Kasa ta maka ’yan kwadagon bisa zargin raina kotu saboda ta ce a baya an hana su shiga zanga-zangar amma suka yi kunnen uwar shegu.

Amma a cewar sanarwar wacce shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, ya fitar, NLC ta ce Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da Kotun Ma’aikata sun ci gaba da yarda ana amfani da su a matsayin “makiya Dimokuradiyya.”

NLC ta ce duk da bayan tattaunawarta da Shugaban Kasa, Bola Tinubu, a ranar Laraba, inda suka yarda su dakatar da zanga-zangar, za su sake dawowa da ita matukar gwamnatin ba ta janye karar ba.

Joe Ajaero ya kuma ce, “daga cikin abubuwan da muka amince da su akwai cewa mun dakatar da zanga-zangar da muka fara ranar Laraba ce saboda mu dada ba gwamnati lokaci domin mu ga kamun ludayinta.

“Amma mun yanke cewa duk ranar da Kotun Ma’aikata ta yi sammacinmu a kan karar da gwamnati ta shigar da mu, za mu tsunduma yajin aikin gama-gari a duk fadin kasa.

“Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta janye wannan karar da ta shigar da mu, idan kuwa ba haka ba, za mu dawo da zanga-zangar da muka dakatar a ranar 14 ga watan Agusta mai zuwa,” in ji Shugaban na NLC.

Gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dai sun fara zanga-zanga ne a fadin Najeriya don nuna bacin ransu kan cire tallafin mai da sauran manufofin tattalin arzikin da suka kira “masu gallaza wa talakawa” da Shugaba Tinubu ya aiwatar tun bayan darewa karagar mulkin Najeriya.