Mafi karancin albashin 54,000 raunin hankali ne —’Yan kwadago
Kungiyar kwadago ta kekashe kasa cewa N615,000 ne za ta amince da shi a matsayin mafi karancin albashi, don haka tayin N54,000 wasa da hankali ne
Kungiyoyon kwadago a Najeriya sun yi watsi ta tayin Gwamantin Tarayya na mafi karancin albashin Naira 54,000 a matsayin wasa da hankali.
Kungiyar ta bayyana tayin N54,000 da gwamnatin ta yi wa ma’aikatan a matsayin mayar da hannun agogo baya a zaman tattaunawan da bangarorin ke yi kan lamarin.
Aminiya ta ruwaito cewa an tashi baram-baram a taron da gwamnati ta kira a ranar Talata domin zama da bangaren ’yan kwadago domin tattauna batun karin mafi karancin albashi.
Aminiya ta ruwaito cewa a taron farko da suka gudanar kungiyar ta yi watsi da tayin Naira 48,000 a matsayin mafi karancin albashi.
- Gwamnati ta gabatar da N54,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi
- Majalisar Kano za ta yi wa dokar masaratu gyaran fuska
Ko bayan zaman ranar Talata kungiyar kwadagon ta tsaya kai da fata cewa Naira 615,000 shi ne mafi karancin albashi da ya kamata a Najeriya.
A taron manema labarai da suka kira bayan sun fice daga taron, shuagaban kungiyar NLC da takwaransa na TUC sun zargi masu kamfanoni da yin kafar ungulu ga kokarin da ake yi na cimma matsaya kan mafi karancin albashi da zai iya rike ma’aikaci a wata.
Kungiyar ta ce duba da halin matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, wasa da hankali ne a yi tunanin Naira 54,000 zai iya rike ma’aikaci da iyalansa har tsawon wata guda.
Sun bayyana cewa sun tsaya a kan N615,000 bayan lissafa abin da zai ishi ma’aikaci mai iyalai mutum shida na tsawon wata guda.
A halin da ake ciki kungiyoyin sun ba bangaren wa’adin zuwa 31 ga watan nan na Mayu ta biya musu bukata, ko su tsunduma yajin aiki.