’Yan kwallo 10 da suka fi samun kudi

Jim kadan bayan an fara kakar wasa ta bana a sassan duniya a makon jiya ne sai Mujallar Forbes da ke bin diddigin yadda ’yan kwallo ke samun kudin shiga a sassan duniya ta kawo rahoton ’yan kwallo 10 da suka fi samun kudi. Kafar sadarwar Naij.com ce ta lalubo bayanin yayin da Aminiya ta […]

’Yan kwallo 10 da suka fi samun kudi

Jim kadan bayan an fara kakar wasa ta bana a sassan duniya a makon jiya ne sai Mujallar Forbes da ke bin diddigin yadda ’yan kwallo ke samun kudin shiga a sassan duniya ta kawo rahoton ’yan kwallo 10 da suka fi samun kudi.

Kafar sadarwar Naij.com ce ta lalubo bayanin yayin da Aminiya ta ci karo da shi a yanar sadarwar Intanent inda kuma ta fassara wa masoya shafin labarin wasanninta kamar haka:

10. Luis Suarez (FC Barcelona). Mujallar Fobes ta kalato cewa dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen shi ne na 10 daga jerin wadanda suka fi daukar albashi da kuma samun kudi a harkar kwallo a duk fadin duniya. Mujallar ta ce tsohon dan kwallon Ajad da ke Holland da kuma Liberpool da ke Ingila yana dibar albashin da suka kai Dala miliyan 16.5 kwatankwacin Naira biliyan 3 da miliyan 630 a shekara. Baya ga haka dan kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 4 da dubu 500 a shekara a wajen yi wa wasu kamfanoni tallace-tallace a lokacin da yake kulob din Liberpool na Ingila.

Sai dai duk da dambarwar da ta sarke dan kwallon a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil bayan an same shi da laifin yin cizo, al’amarin da ya sa wadansu kamfanoni suka daina yin hulda da shi, amma duk da haka dan kwallo ne na goma a jerin wadanda suka fi samun kudi a harkar kwallo.

9. Sergio Aguero (Manchester City): Serrgio Aguero, haifaffen Ajantina da yanzu haka yake buga wa kulob din Manchester City da ke Ingila kwallo shi ne na 9 a jerin ’yan kwallon da suka fi daukar kudi. An kiyasta dan kwallon yana daukar albashin da suka kai Dala miliyan 17.9 kwatankwacin Naira Biliyan 3 da miliyan 980 a shekara. Sannan yana yi wa kamfanoni tallan da ta kai Dala miliyan 7 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 540 a shekara.

8. Radamel Falcao (Chelsea FC): Duk da cewa dan kwallon bai tabuka abin kirki a kulob din Manchester United da ke Ingila a bara ba, kimarsa a wajen samun kudin shiga ba ta yi kasa ba. dan kwallon da tuni ya koma kulob din Chelsea na Ingila a kakar wasa ta bana an kiyasta yana samun Dala miliyan 25.9 a shekara. Dala miliyan 21.9 daga cikin kudin a matsayin albashi yayin da Dala miliyan hudu kuma a matsayin kudin tallace-tallace ga kamfanoni da dama.

7. Wayne Ronney (Manchester United). Wayne Ronney dai dan kwallon Manchester United da ke Ingila ne. A jerin ’yan kwallon da suka fi samun kudi a duniya shi ne na 7. An ruwaito dan kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 26.9 a shekara. Daga adadin kudin Dala miliyan 19 da miliyan 9 a matsayin albashinsa, yayin da yake samun Dala miliyan 7 a matsayin kudin yin talla. Kafofin watsa labarai sun yi ta rade-radin dan kwallon zai koma kulob din PSG a kakar wasa ta bana, amma da alama dan kwallon ba zai canza sheka ba.

6. James Rodriguez (Real Madrid CF): James dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen wanda ya koma kulob din daga na Monaco na Faransa a bara, yanzu haka shi yake sanya rigar kwallo mai lamba 10 a kulob din na Madrid. An ruwaito sai da Madrid ta ajiye wa Monaco zunzurutun Dala miliyan 108 kafin ta saye shi daga Monaco. Mujallar Forbes ta ruwaito yanzu haka dan kwallon yana daukar albashin da suka kai Dala miliyan 29 a shekara. Dala miliyan 24.5 sun zama albashinsa yayin da Dala miliyan 4 da miliyan 500 suka kasance kudaden tallar da yake yi wa wadansu kamfanoni a sassan duniya.

5. Neymar Jr. (FC Barcelona): Neymar dai haifaffen Brazil ne. Yanzu haka shekarun dan kwallon 23, kuma ana hasashen dan kwallon zai iya zama Gwarzon dan kwallon duniya nan da wadansu shekaru masu zuwa. Mujallar ta ce an kiyasta yana dibar albashin da ya kai Dala miliyan 31 kwatankwacin Naira biliyan 6 da miliyan 820 a shekara. Sai dai daga cikin wannan adadi an kiyasta yana samu Dala miliyan 17 ne daga wajen yi wa kamfanoni tallace-tallace. Da alama dan kwallon zai fi kowane dan kwallo haskakawa a nan gaba idan ya cigaba da nuna kwazo kamar yadda masana harkar kwallo suka nuna.

4. Gareth Bale (Real Madrid CF): Gareth Bale shi ne dan kwallon da ya fi kowane tsada a tarihin cinikin ’yan kwallo a duniya. Sai da kulob din Real Madrid ya ajiye Fam miliyan 85 kwatankwacin Naira Biliyan 31 da miliyan 875 kafin ta saye shi daga kulob din Tottenham da ke Ingila shekaru biyu da suka wuce. An kiyasta dan kwallon yana daukar albashin da ya kai Dala miliyan 35 kwatankwacin Naira biliyan 7 da miliyan 700 a yanzu. Sai dai daga kudin an ruwaito yana samun Dala miliyan 9 da dubu 500 ne daga bangaren tallace-tallace. Kenan tsuran albashinsa ya kasance Dala miliyan 25 da dubu 500.

3. Zlatan Ibrahimobic (PSG): Haifaffen Sweden, Zlatan Ibrahimobic dai shi ne na 3 a jerin ’yan kwallon da suka fi samun kudi a bangaren kwallo. Yanzu haka yana kwallo ne a kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kuma an kiyasta yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 33.1 a shekara. Daga ciki kuma yana samun akalla Dala miliyan 6 ne a bangaren tallace-tallace.

2. Lionel Messi: (FC Barcelona): Lionel Messi, dan kwallon da ake ganin babu kamarsa a duniya shi ne na biyu a halin yanzu a jerin ’yan kwallo 10 da suka fi daukar albashi. Mujallar ta ce dan kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 73 a shekara kwatankwacin Naira Biliyan 160 da miliyan 60 a shekara. Sai dai Dala miliyan 51.8 daga cikin kudin yana samun su ne daga bangaren tallace-tallace ga kamfanoni daban-daban a duniya.

1. Cristiano Ronaldo: (Real Madrid CF): dan kwallon Madrid kuma haifaffen Sifen, Ronaldo shi ne Mujallar Forbes ta ruwaito a matsayin dan kwallon da ya fi kowane dan kwallo samun kudi a fadin duniya. An ce dan kwallon yana dibar kudin da suka kai Dala miliyan 79.6 a shekara kwatankwacin Naira biliyan 175 da miliyan 120. Sai dai dan kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 52.6 ne daga bangaren yin tallace-tallace daga cikin adadin kudin da yake samu. Masu wasan damben boksin Floyd Mayweather da Manny Packuaiao ne kadai aka ruwaito suka fi Ronaldo daukar albashi a duk fadin duniya. Yanzu haka dan kwallno ne yake rike da kambun Gwarzon dan kwallon duniya da ya lashe sau biyu a jere, amma Lionel Messi ne ya kafa tarihin dan kwallon da ya taba lashe kyautar sau hudu a jere. Sannan a shekaranjiya Laraba ne Hukumar FIFA ta fitar da jerin ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon duniya ta bana ciki har da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.