’Yan kwallon Brazil na shan caccaka saboda rashin halartar jana’izar Pele
Sun zabi nuna alhinin rashinsa ta shafukansu na sada zumunta.
Taurarin kwallon kafar Brazil na shekarun baya da na yanzu suna shan caccaka daga magoya bayansu saboda rashin halartar jana’izar Pele, inda suka zabi nuna alhinin rashinsa ta shafukansu na sada zumunta.
A ranar Talatar da ta gabata, aka yi jana’izar zakaran Gasar Kofin Duniya sau uku a garinsa Santos, taron da mutane fiye da 230,000 suka halarta a filin wasa na Vila Belmiro.
Magoya baya sun yi tsammanin tsofaffin ’yan wasan kungiyar Santos kamar Neymar, Rodrygo da Giovanni za su halarci jana’izar Pele, amma ba a gansu ba.
An kuma yi fatan ganin manyan ‘yan wasan Brazil da suka yi ritaya irinsu Zico, Romario, Ronaldo Nazario, Ricardo Kaká da Ronaldinho, amma su ma suka watsa wa magoya baya kasa a ido.
Tuni dai shafukan sada zumuntar ‘yan wasan na yanzu da tsaffinsu suka cika da korafi daga fusatattun magoya bayansu bayan da aka binne Pele.
Wani abu da ya dauki hankali kuma shi ne yadda babu daya daga cikin ’yan wasan tawagar kasar Brazil da ta lashe Gasar Kofin Duniya a shekarar 2002 da ya halaci taron na binne Pele.
Daya daga cikinsu kuma tsohon dan wasan tsakiya, Kaka yafi shan suka, saboda yadda a wata hira da manema labarai a watan Disamba, ya taba korafi kan cewa ’yan Brazil ba sa girmama fitattun ‘yan wasan da suka gabace su, kamar yadda suke girmama na kasashen waje.