’Yan kwallon Kaduna United sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashin watanni 12

A ranar Litinin da ta gabata ne daukacin ’yan kwallon Kaduna United suka gudanar da zanga-zangar lumana saboda rashin biyansu albashin watanni 12.  ’Yan kwallon sun gudanar da zanga-zangar ce a harabar Ma’aikatar kula da wasanni da matasa ta Jihar Kaduna.  A lokacin da suke hira da manema labarai ’yan kwallon sun ce kimanin watanni […]

’Yan kwallon Kaduna United sun yi zanga-zangar rashin biyansu albashin watanni 12

A ranar Litinin da ta gabata ne daukacin ’yan kwallon Kaduna United suka gudanar da zanga-zangar lumana saboda rashin biyansu albashin watanni 12.  ’Yan kwallon sun gudanar da zanga-zangar ce a harabar Ma’aikatar kula da wasanni da matasa ta Jihar Kaduna.  
A lokacin da suke hira da manema labarai ’yan kwallon sun ce kimanin watanni 12 kenan rabon da a biyasu albashi.
daya daga cikin ’yan kwallon wanda ya ki barin a ambaci sunansa ya shaida wa ’yan jarida  cewa sun gudanar da zanga-zangar ce don janyo hankalin gwamnatin jihar na rashin biyan albashin watanni 12 da kuma wadansu daga cikin alawus-alawus din su.
Ya ce su ma mutane ne kamar kowa don haka suna bukatar kudin da za su gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.  “Mun kwashe tsawon lokaci muna buga wasa ba tare da sisin kwabo ba, ta yaya ake tsammanin za mu rayu a cikin irin wannan yanayi?”, inji shi.
“Da yawa daga cikinmu muna da iyalan da suka dogara a kanmu don haka muke neman a biyamu hakkokinmu”.
Da yawa daga cikin ’yan kwallon sun danganta rashin tabuka abin-a-zo-a-gani da kulob din ke yi  a kakar wasa ta bana a kan rashin biyan hakkokinsu a kan lokaci.
Ya zuwa yanzu, Kaduna United tana daga cikin kungiyoyin da ke sahun baya a jadawalin gasar rukunin firimiya na kasa.
Sai dai a nasa bangaren a tattaunawarsa da Aminiya ta waya, Janar Manajan kulob din Kaduna United, Garba Lawal ya bayanna mamakin yadda ’yan kwallon suka gudanar da zanga-zangar ba tare da saninsa ba.
Ya ce da yawa daga cikin ’yan kwallon suna zarginsa da laifin kin biyansu bayan gwamnati ta ba shi kudi amma ya godewa Allah da yanzu suka fahimci gaskiyar al’amari.
“A mafi yawan lokuta na sha ba ’yan kwallon hakuri a kan rashin biyansu hakkokinsu kuma ina ba su tabbacin komai zai gyaru amma an wayi gari sun yi biris da shawarar da na ba su sun shiga zanga-zangar lumana amma ban ga laifinsu ba don hakkinsu suke nema”.
“Sai dai na tabbata yanzu sun fahimci inda aka sanya gaba, wadanda ke zargin an ba ni kudi na ki ba su ne, yanzu sun tabbatar abin ba haka yake ba”.
Sai dai Garba Lawal ya bayar da tabbacin babu dan kwallon da za a hukunta saboda shiga zanga-zangar lumana da suka yi amma duk da haka ya shawarce su da su cigaba da hakuri nan gaba kadan komai zai daidaita.
Sai dai kyaftin Emmanuel Ambrose ya bayar da tabbacin ’yan kwallon za su cigaba da buga wasa duk da rashin biyansu albashin.
Rahoton da muka sanu ya nuna tun da shekarar da muke ciki (2014) ta kama kawo yanzu ba a biya ’yan kwallon albashi ba.  Kuma a shekarar bara ma suna bin albashin watanni uku.