’Yan kwallon kwandon Najeriya sun haye gasar Olamfik
A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan kwallon kwando na Najeriya bangaren maza da aka fi sani da D’Tigers suka yi rawar gani bayan sun haye zuwa gasar Olamfik da za a yi badi a Tokyo ta kasar Japan. Sun samu nasarar haka ne bayan sun lallasa mai masaukin baki a Gasar Kwallon Kwando ta […]
A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan kwallon kwando na Najeriya bangaren maza da aka fi sani da D’Tigers suka yi rawar gani bayan sun haye zuwa gasar Olamfik da za a yi badi a Tokyo ta kasar Japan.
Sun samu nasarar haka ne bayan sun lallasa mai masaukin baki a Gasar Kwallon Kwando ta Duniya da aka yi China.
D’Tigers ta lallasa kasar China ne da ci 86-73 inda hakan ya sa ta zama ta farko a Nahiyar Afirka wajen hayewa gasar ta Olamfik.
Tun farko an shirya za a gudanar da gasar kwallon kwando ta duniya ce a bara a China amma aka daga zuwa bana saboda wasu dalilai. Wannan ne karo na farko da aka taba daga gasar tun bayan da aka fara ta a 1967.
Shekara biyu ke nan da D’Tigers ta lashe gasar kwallon kwando ta Afirka a karon farko.
Tuni Shugaban Kasa Buhari ya aika da sakon taya murna ga kungiyar inda ya nemi su ci gaba da nuna kwazo don lashe lambar zinare a gasar Olamfik mai zuwa a Tokyo.