’Yan kwallon Sardauna Babes biyu sun arce a lokacin da kulob din ya kai ziyara Turai

Wani abin kunya ya sake faruwa a karshen makon jiya a lokacin da biyu daga cikin ’yan kwallon Sardauna Babes da ke Kano suka arce a wata ziyara da kulob din ya kai kasar Sweden don yin wasannin sada zumunta.Kamar yadda labarin da kafar watsa labarin wasanni ta AfricanFootball.com ta kalato ya nuna ’yan kwalo […]

’Yan kwallon Sardauna Babes biyu sun arce a lokacin da kulob din ya kai ziyara Turai
’Yan kwallon Sardauna Babes biyu sun arce a lokacin da kulob din ya kai ziyara Turai

Wani abin kunya ya sake faruwa a karshen makon jiya a lokacin da biyu daga cikin ’yan kwallon Sardauna Babes da ke Kano suka arce a wata ziyara da kulob din ya kai kasar Sweden don yin wasannin sada zumunta.
Kamar yadda labarin da kafar watsa labarin wasanni ta AfricanFootball.com ta kalato ya nuna ’yan kwalo biyun da suka yi batar dabon  su ne Sunday Ajala da kuma Kabiru Musa.  Amma tuni sauran ’yan kwallon suka dawo Najeriya ba tare da sun yi kwallo ba.
Shi dai kulob din an shirya masa zai yi wasannin sada zumunta da kulob da dama ne a Sweden ciki har da wasan da kulob din zai yi da na Kalmar kafin daga bisani wadanda suka shirya wasan su canza ra’ayi.
An ruwaito cewa wadanda suka shirya wasan, sun ware wa kulob din Naira miliyan 12 na kudin jirgi da na otel da kuma na alawus-alawus din ’yan kwallo ne amma sai kulob din ya aika da ’yan kwallo tara kacal maimakon 11 ko fiye da haka.  Sannan daga cikin taran ne biyu daga ciki suka arce yayin da sauran bakwai suka koma gida.
Rahoton ya ce daukacin ’yan kwallon da jami’ansu sun komo gida ne ba tare da sun yi wasa ko sau daya ba saboda sabanin da aka samu a tsakanin wadanda suka shirya gasar da kuma jami’an Najeriya da kuma na kulob din.
Ya zuwa wannan lokaci, ba a gano wurin da ’yan kwallon suka makale ba, amma dai an tabbatar sun makale a kasar ce don samun kulob din da za su cigaba da yi wa kwallo.
Idan za a tuna, dan kwallon gaba a kulob din Flying Eagles Bernard Bulbwa ya shiga matsala bayan kulob dinsa na da Shuttle Sports Academy da ke Najeriya ya kai karar kulob din Esperance na Tunisiya  gaban Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) na rashin biyan Dala dubu 180 kwatankwacin Naira miliiyan 38 da dubu 700 a matsayin kudin canza sheka ga kulob din.  Kulob din ya ce har yanzu ba su karbi sisin kwabo daga wajen Esperance a matsayin kudin canza shekar Bulbwa ba kuma tuni dan kwallon ya koma Tunisiya.
Akwai yiwuwar FIFA ta hukunta kulob din Esperance idan ta same shi da laifi a kan haka.