’Yan kwamitin rubuta tsarin mulkin Masar sun fice saboda kame masu zanga-zanga
Waklilai 10 na kwamitin rubuta sabon tsarin mulki a kasar Masar sun fice daga zauren da suke aiki, domin nuna rashin amincewa da kama daruruwan masu zanga-zanga a birnin Alkahira. Masu zanga-zangar an kama su ne a birnin bayan da suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar da ta takaita wa jama’a yin […]
Waklilai 10 na kwamitin rubuta sabon tsarin mulki a kasar Masar sun fice daga zauren da suke aiki, domin nuna rashin amincewa da kama daruruwan masu zanga-zanga a birnin Alkahira. Masu zanga-zangar an kama su ne a birnin bayan da suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar da ta takaita wa jama’a yin zanga-zanga a kasar.
Kakakin kwamitin rubuta tsarin mulkin ya shaida wa gidan redion BBC Landan cewa ya samu tabbacin za a sako mutanen cikin gaggawa. Kuma ya ce za a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan tsarin mulkin kafin karshen wannan shekara.
Wannan shi ne babban mataki na farko na sake mayar da mulki hannun farar hula, tun bayan juyin mulkin soja da ya kawar da Shugaba Muhammad Mursi mai ra’ayin addini a watan Yulin da ya gabata.
Firayi Ministan Riko na kasar Hazem Beblawi ya bayyana kuri’ar jin ra’ayin jama’ar a matsayin “mafi muhimmancin lokaci” ga Masar. Daga farko ya ce za a gudanar da kuri’ar ce a watan Janairun badi.
Ana sa ran zaben ’yan majalisa da na shugaban kasa za su biyo bayan kuri’ar jin ra’ayin jama’ar da za ta amince da tsarin mulkin.
Wani kwamitin mutum 50 wadanda kalilan daga cikinsu masu kishin addini ne, sun fara aikin gyara tsarin mulkin da Mursi ya gabatar tun a watan Satumba. Kuma sojojin kasar sun ba kwamitin kwana 60 ya kammala aikinsa.
Magoya bayyan Mursi suna ci gaba da zanga-zangar adawa da mahukuntan kasar tare da neman a maido shi kan kujerarsa. Kuma sun ki amincewa da halaccin gwamnatin kasar, kuma ana jin za su yi kamfe din nuna adawa da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar.
Masu rajin kare hakkin dan Adam sun yi ta zanga-zanga domin adawa da sabuwar dokar da ta ce sai an nemi amincewar ’yan sanda kafin a gudanar da taron da ya wuce na mutum 10.
A ranar Talatar da ta gabata, ’yan sandan kwantar da tarzoma sun kama fiye da mutum 25 a Alkahira, kuma sun yi amfani da motar ruwan zafi wajen tarwatsa zanga-zangar.
kungiyoyin kare hakkin dan Adam, sun ce sabuwar dokar wani babban koma-baya ne ga ’yancin haduwar jama’a a kasar Masar.