’Yan kwangila na buƙatar Naira tiriliyan 1.35 su kammala titin Kano zuwa Abuja
Yanzu kuwa gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya ce Kamfanin gine-gine na Julius Berger da ke kwangilar babban titin Kano zuwa Abuja, na neman naira tiriliyan 1.35 domin kammala aikin.
Da yake magana a wani taro ranar Alhamis tare da daraktocin ma’aikatar ayyukan a Abuja, babban birnin Najeriya, ministan ya ce titin da farko an ware naira biliyan 165 wanda aka ƙara kuɗin zuwa naira biliyan 654.
- Kotun Koli ta hana madugun adawar Senegal Ousmane Sonko tsayawa takara
- Har yanzu gas din girki na gagarar talaka bayan wata daya da alkawarin gwamnati
Sai dai ya ce a yanzu kuwa gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.
Ana iya tuna cewa, tun a shekarar 2017 ce Gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar amma sai a 2018 aka soma aikin.
Ya kamata a kammala titin cikin shekarar 2021 wanda ɗaya ne daga cikin ayyukan gwamnatin Buhari.
Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a 2023, inda a yanzu dai an kammala fiye da rabin aikin titin.
Ya kara da cewa ma’aikatar tana kuma nazari kan shimfiɗa titin kilomita 40 na farko da rukunin Kamfanin Dangote zai gina a karkashin Shirin Bayar da Haraji.
Ya ce galibin wurin da aikin ya rage yana buƙatar a yi masa zubin kankare saboda wuri ne da ya kasance kwarmi mai tara ruwa.
Ya kuma bayyana cewa “duk rintsi za mu kammala aikin a bana.”