’Yan Kwankwasiya a Nasarawa sun nemi Buhari ya janye wa Kwankwaso

Shugaban wata sabuwar kungiya mai suna ‘Kwankwasiyya 2015 Insha Allah’ a Jihar Nasarawa kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar ACN reshen jihar Alhaji Suleiman Alhassan ya yi kira ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya janye daga batun tsayawa takara a zabe mai zuwa ya mara wa Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso baya. Alhaji […]

’Yan Kwankwasiya a Nasarawa sun nemi Buhari ya janye wa Kwankwaso
’Yan Kwankwasiya a Nasarawa sun nemi Buhari ya janye wa Kwankwaso

Shugaban wata sabuwar kungiya mai suna ‘Kwankwasiyya 2015 Insha Allah’ a Jihar Nasarawa kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar ACN reshen jihar Alhaji Suleiman Alhassan ya yi kira ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya janye daga batun tsayawa takara a zabe mai zuwa ya mara wa Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso baya.
Alhaji Suleiman Alhassan ya yi wannan kira a wurin wani gangami da kungiyar ta gudanar a Lafiya, inda ya ce akwai bukatar Janar Buhari ya janye ya mara wa Gwamna Kwankwaso baya idan aka yi la’akari da ayyukan da Kwankwaso ke gudanarwa a Jihar Kano da kuma farin jini da yake da shi a gurin talakawa.
Ya ce sun kafa kungiyar ce da nufin yin kira ga Gwamna Kwankwaso ya fito takarar Shugaban kasa a shekarar 2015, a cewarsa a halin yanzu shi ne kadai a Arewa ya cancanci tsayawa takarar kujerar.
Ya ce kungiyar tana shirye-shiryen bude rassanta a kananan hukumomin jihar don jawo ra’ayin Gwamnan ya tsaya takara tare da nema masa goyon bayan jama’a.
Ya bukaci al’ummar jihar da kasa baki daya su fito su hada karfi don goya wa Kwankwaso baya, ta yadda za a ceto kasar nan daga mugun shugabancin da Jam’iyyar PDP ke yi a kasar nan.
Da suke tofa albarkacin bakinsu shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar kira suka yi ga masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC su janye wa Kwankwaso su kuma yi tafiya tare da shi don samun nasara a shekarar 2015, kuma sun yi alkawarin ci gaba da wayar da kan al’ummominsu don su shiga kungiyar a dama da su.