’Yan majalisa 17 sun fice daga ADC zuwa NDC
A zaman majalisar, an sanar da cewa wani dan majalisa, Leke Abejide, ya fice daga ADC zuwa jam’iyyar APC.
Majalisar Dokoki ta Kasa
Akalla ’yan Majalisar Wakilai 17 sun sauya sheƙa daga Jam’iyyar ADC zuwa NDC.
An sanar da sauyin nasu ne a zaman majalisar wakilai na ranar Talata.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sauyin sheƙar wasu manyan ’yan siyasa, ciki har da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadanda suka koma NDC a baya-bayan nan daga ADC.
Sauyin na kara nuna yadda siyasar zaben 2027 ke daukar sabon salo, yayin da jam’iyyun adawa ke sake fasalin kansu.
- Kotu ta rushe zaɓen shugabannin ADC na Adamawa
- Juyin mulki: Mutum 2 sun amince sun san da shirin kifar da gwamnati
Haka kuma, a zaman majalisar, an sanar da cewa wani dan majalisa, Leke Abejide, ya fice daga ADC zuwa jam’iyyar APC.
Daga cikin ’yan majalisar da suka koma NDC akwai Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi da Peter Aniekwe.
Sauran su ne Mukhtar Zakari, George Oluwande, Munachim Umezuruike, Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da Abdulhakeem Ado.
Ana sa ran karin bayani kan lamarin nan gaba.