‘Yan majalisa 26 sun fice daga APC a Ogun
‘Yan majalisar dokokin jihar Ogun 26 ne suka fice daga jam’iyya mai mulki ta APC inda suka koma jam’iyyar adawa ta APM. Majiyarmu ta gano cewa, wadanda suka fice daga jam’iyyar su na cikin fusatattun ‘yan takarar jam’iyyar wanda suka ce, jam’iyyar APC ba ta yi masu adalci ba, lokacin zaben fidda gwani na APC […]
‘Yan majalisar dokokin jihar Ogun 26 ne suka fice daga jam’iyya mai mulki ta APC inda suka koma jam’iyyar adawa ta APM.
Majiyarmu ta gano cewa, wadanda suka fice daga jam’iyyar su na cikin fusatattun ‘yan takarar jam’iyyar wanda suka ce, jam’iyyar APC ba ta yi masu adalci ba, lokacin zaben fidda gwani na APC da aka yi ranar 7 ga Oktoba 2018.
Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya zargin shugaban APC Adams Oshiomhole akan yunkurin raba kan ‘yan siyasar jihar.