’Yan Majalisa ba sa kokarin da ya dace – Farfesa Bakin Zuwo
Wani masanin harkar man fetur kuma mai sharhi a kan al’amuran siyasa, Farfesa Baba Jibrin Bakin Zuwo ya zargi ’yan Majalisar Tarayya da gazawa wajen aiwatar da aikinsu na kafa dokoki masu kawo tasiri a kan tsare-tsaren gwamnati da kasafin kudi da aiwatar da shi yadda ya kamata.Farfesa Baba Bakin Zuwo ya bayyana haka ne […]
Wani masanin harkar man fetur kuma mai sharhi a kan al’amuran siyasa, Farfesa Baba Jibrin Bakin Zuwo ya zargi ’yan Majalisar Tarayya da gazawa wajen aiwatar da aikinsu na kafa dokoki masu kawo tasiri a kan tsare-tsaren gwamnati da kasafin kudi da aiwatar da shi yadda ya kamata.
Farfesa Baba Bakin Zuwo ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin taron Rundunar Siyasa ta Matasan Najeriya a Kano, inda ya ce gogayyar da ya samu a kasashen Ingila da Saudiyya da kuma Oman inda ya yi aiki, akwai bambanci mai yawa a tsakanin majalisunsu da ta Najeriya.
Ya ce yana takaicin yadda Najeriya ta dogara kacokam a kan man fetur wajen samun kudaden shiga da rashin daidaito wajen raba arzikin kasa, inda ake fifita Kudu a kason kudin man da ake sayarwa. “Ina takaicin ganin yadda ake ba jihohin Kudu kudi har ma da na man da ke cikin teku, wanda mallakar kasa ne gaba daya kuma babu inda ake yin haka a duniya, sai a nan kasar,” inji shi.
Farfesa Bakin Zuwo ya ce ya kamata a mai da hankali a kan hanyoyin bunkasa tattalin arziki da ma’adinai da ke Arewa da aka kyale su kara-zube ba tare da an tono su ba.
Ya ce dalilin rashin ingantaccen shugabanci da kyakkyawan tsari, kasashen da suka taso tare da Najeriya a shekarun 1970 a yankin Larabawa da Asiya duk sun ci gaba sun bar ta a baya.
Farfesan ya ba da shawarar cewa, ya kamata Najeriya ta bullo da hanyoyin samar da man mota da na injunan masana’antu ta hanyar sarrafa tsirrai da kayan amfanin gona.
Ya ce gyara tattalin arzikin ne kadai zai samar da sana’o’i ga tarin matasan da suke kammala karatu ba su da abin yi.