’Yan majalisa da zargin neman mata

Zargin da gwamnatin Amurka ta yi na yunkurin yin fyade da neman mata ga wadansu ’yan Majalisar Wakilai babban al’amari da ya kamata a tsaya a yi binicken kwakwaf a kai duk da cewa akwai alamar rudu a ciki. A cikin wata wasika da Jakadan Amurka a Najeriya Mista James Entwistle ya aike ga Shugaban […]

’Yan majalisa da zargin neman mata
’Yan majalisa da zargin neman mata

Zargin da gwamnatin Amurka ta yi na yunkurin yin fyade da neman mata ga wadansu ’yan Majalisar Wakilai babban al’amari da ya kamata a tsaya a yi binicken kwakwaf a kai duk da cewa akwai alamar rudu a ciki. A cikin wata wasika da Jakadan Amurka a Najeriya Mista James Entwistle ya aike ga Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara a ranar 9 ga Yunin bana, ya zargi Mark Gbillah (APC, Benuwai) da Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Garba Gololo (APC, Bauchi) da neman yin jima’i a lokacin da suka ziyarci birnin Clebeland da ke Jihar Ohio a baya-bayan nan domin halartar taron da cibiyar kula da shugabanci International bisitors Leadership ta shirya. Suna daga cikin ’yan majalisa bakwai da suka halarci wannan taro.
A cewar Entwistle, ana zargin Gololo da kai runguma ga mai sharer dakin otel dinsa, yayin da ake zargin Gbillah da Ikon da ma’aikatan otel din su taimaka musu wajen nemo musu karuwai. Dogara ya bayyana zargin da babba kuma ya nuna damuwa kan yadda ’yan Najeriya da dama suka yanke wa ’yan majalisar hukuncin masu laifi ba tare da lura da illar da hakan zai yi ga kasar kanta ba.
’Yan majalisar uku sun nuna damuwa kan yadda lamarin ya zama babban labara na tsawon kwanaki da kuma yadda ya zubar musu da mutunci. Sun bukaci shugabannin majalisar su gudanar da binciken a bainar jama’a kan lamarin.   dan majalisa Samuel Ikon ya ma rubta wasika ne ga Jakada Entwistle yana barazanar zai dauki matakin shari’a a kotunan Najeriya da Amurka. Ya ce ba ya da lafiya a lokacin tafiyar don haka ba zai iya jima’i ba balle ya nema. Ya ce ba ya da sauran zabi face ya garzaya kotu idan jakadan ya ki wanke sunansa daga zargin.
Ba karamin abu ba ne zai sa Jakadan Amurka ya rubuta irin wannan wasika ga Dogara. kila Amurkawa sun gudanar da nasu bincikem kafin su rubuta waccan wasika, domin wannan lamari yana iya illa ga dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Kuma zai iya kawo cikas ga horarwar da Amurka ke ba ’yan majalisa daga Najeriya in aka lura da rashin yarda da juna da wannan batu zai kawo. Duk da haka akwai rudu ko rikitarwa a wani bangare na daukacin lamarin.  Na farko ’yan majalisar sun halarci wannan taro na Ohio ne wata biyar da suka gabata. Don haka an dauki dogon lokaci kafin a gudanar da saukakar bincike kan irin wannan lamari. Kuma idan ’yan majalisar wadanda ba su da kariyar diplomasiyya ta gurfana a gaban shari’a, sun aikata irin wannan laifi na rungumar mai sharer daki, Amurkawan suna iya gabatar da wanda ake zargi a kotu tun a can kuma nan take maimakon su kyale shi ya dawo gida daga baya su kawo wasika ga Shugaban Majalisar.
Daidai ne da Shugaban Majalisa Dogara ya nuna damuwa kan yadda ’yan Najeriya da dama suka ruga suka yanke hukunci cewa ’yan majalisar sun aikata abin da ake zarginsu. Abin takaici hakan na faruwa ne sakamakon halayyar wadansu ’yan majalisar marasa kyau hatta a nan cikin gida. Da dama daga cikinsu suna rayuwa c eta facaka da kudi da nuna gadara, suna ganin za su iya yin komai su sha. Mutumin da koyaushe yake take doka da ka’ida a kasarsa yana iya aikata haka a waje.
Ba cewa muke yi wadanda ake zargin sun aikata laifin ba. A’a wajibi ne a nuna shakku kan hakan ganin cewa dukkansu sun musanta zargin. Wannan yana iya zama wata jarrabawa ga ’yan majalisar, wadanda dukkansu suna da iyalai da abokai. Kuma bai kamata shugabannin majalisar su yi ta jan kafa kan batun ba, kuma wajibi ne su gudanar da binciken ba sani ba sabo. Idan ’yan majalisar suna son gurfanar da Mista Entwistle kan wannan zargi suna iya yin haka bayan binciken majalisar ya wanke su. Yanzu dai an zuba wa Majalisar Wakilai ido kan ta gudanar da cikakken bincike ta yadda ’yan Najeriya za su san gaskiyar lamarin.
Ba tare da nuna cewa ’yan majalisar sun aikata laifin dab ake zarginsu ba, wannan bakin lamari tunatarwa ce ga dukkan ma’aikata da jami’an gwamnati da sauran ’yan Najeriya cewa a duk lokacin da suka tafi wata kasar waje su jakadu ne na kasar nan, don haka su rika yin taka-tsantsan don kada su sanya kansu a cikin wani lamari da zai jawo musu abin kunya ko ga kasarsu.