’Yan majalisa kun bai wa talakawa kunya
Editan Aminiya, don Allah ba ni dama in yi tsokaci akan sayen motocin da ‘yan majalisar tarayya suka yi mallakar kamfanin fijo (peugeot) kirar 508 akan kudi Naira miliyan 10 ga kowane dan majalisar wakilai, su 360. Haka su ma ‘yan majalisar dokoki su 109 sun sayi makamantan wadannan motocin kimanin guda 35 ga kowane […]
Editan Aminiya, don Allah ba ni dama in yi tsokaci akan sayen motocin da ‘yan majalisar tarayya suka yi mallakar kamfanin fijo (peugeot) kirar 508 akan kudi Naira miliyan 10 ga kowane dan majalisar wakilai, su 360. Haka su ma ‘yan majalisar dokoki su 109 sun sayi makamantan wadannan motocin kimanin guda 35 ga kowane sanata da ke fadin Najeriya, a kan kudi Naira miliyan 35 kowacensu. To a gaskiya mu talakawan Najeriya kun ba mu kunya, kuma kun nuna mana cewa, ba matsalolin talakawa ba ne a gabanku ganin yadda kuka kasa yin wani hobbasa wajen kirkiro da wasu dokoki da za su kawo wa talakawan kasar nan saukin rayuwa. Bayan haka muna amfani da wannan damar mu shaida muku cewa, duk wani dan majalisa da ke wakiltarmu a majalisar tarayya za mu sa kafar wando guda da ku, tunda mun gano cewa, yanzu ba mu kuke wakilta ba, aljihunanku ne, kuke wakilta. Sannan muna yi wa Shugaba Muhammadu Buhari addu’a a kan samun nasarar taimaka wa talakawan Najeriya, ta yadda za su fita daga cikin halin kaka-ni-ka-yi da suke ciki.
Daga Kwamared Nura Bello Daraja Kaset Gusau dan kishin kasa 07036007481. [email protected]
Maratanin Janye lefe a hidimar aure
Salam, Sani na ga maganar da ka yi a jaridar Aminiya ta a janye lefe a aure, amma ka manta ba ka yi maganar kayan daki da suka hada da gado da kujeru da sauransu ba .Ko kai ba ka aurar da yarinya ba ne? Ahmed A. Bichi.
Jinjina ga Abdul’azeez Lawal danyari
Malam Abdul’azeez Lawal danyari. Salam Edita ku yi hakuri ku taimake mu, mu yi godiya a kan motocin da ya saya a lokacin yana shugaban karamar hukluma a shekarar 2007. Ba don wadannan motocin ba, da ’ya’yan mu mata ba za su iya zuwa makaranta ba yanzu,
Daga Yusuf jikan Jaji Malumfashi 08064939999.
Jaje ga Rarara
Muna mika jajenmu gareka.A kan fashin da wasu batagari suka yi maka. Allah ya kare ka, tare dukkan ’yan Najeriya amin.
Daga Musa Kaliyos Kofar Yamma Dambatta.08066988910
Ta.aziyya ga ma’aikacin Aminiya
Aminiya ku ba ni dama domin mika sakon ta’aziyyata ga ma’aikacinku, wato Bashir Yahuza Malunfashi dangane da rasuwar mahaifiyarsa, wato hajiya A’isha (iya) tare da addu’ar Allah jikanta da rahama, Ya sa Aljanna ta zama makomarta amin.
Daga Alhaji Zubairu Garabasa Kazaure.
A dauki kurame da bebaye aikin tsaro
Edita.don Allah ka isar da sakona ga Shugaba Buhari da Janar Mansur dan Ali, domin su amince a rika daukar wadanda ba sa ji sosai aikin soja da dansanda, matukar sun nema. Ya ya za a yi a ce kawai sai masu ji sosai kawai za a dauka aikin tsaro, kamar soja da dansanda da kwastamda Jami’an tsaron farin kaya da sauransu. Hatta ni da nake magana ina son aikin soja ko dansanda ko kwastam sai dai kash ba za a dauke ni ba, saboda ba na ji sosai. Don Allah a tausaya mana in mun nema a daukemu. Domin a cikinmu akwai masu Digiri da babbar difuloma (HND) da shaidar ilimi ta kasa (NCE) da difuloma da shaidar kammala sakandare (SSCE) da sauransu..
Daga.Nazifi Aliyu GGW Jigawa State..
Kira ga Gwamna el-Rufa’i
Don Allah Gwamna Malam Nasiru el-Rufa’i ka taimaka ka sa a fara saka sababbin ’yan fansho su fara karbar fanshon wata-wata (monthly pension), tunda ka zo wata 11 ba a taba biyan sababbin ’yan fansho ba, a kananan hukumomi.
Daga Abdullahi Tudun Wada Makarfi 08100105543.
Jinjina ga wakilin Aminiya a Bauchi
Salmun alaikum. Dubun gaisuwa zuwa ga ma’aikatan Aminiya gaba dayanku. Gaisuwa da jinjina ga Hamza Aliyu Bauchi, wakilin Aminiya, saboda namijin kokarin da ya yi, inda ya ziyarci unguwar bayan gari a Bauchi. Allah cikin ikonsa ya yi sanadiyyar ceto Safiya daga muguwar sana’a da gaisuwa zuwa Alhaji babanmu Abubakar Usman Allah ya kara daukaka.
Daga Garba A Ismaila Kyari, Jihar Jigawa.
Godiya ga Buhari
Daga jama’ar Barno mun gode wa Allah kuma mun gode wa shugabanmu Buhari domin mun gani a kasa Boko Haram sun kusa karewa. Lallai kai ne tunkwal uwar daka. Daga Mustapha Iinspecto dutse.
Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba
Salam Aminiya na yi wannan karim magana ne domin ganin irin halin da talaka yake ciki a yanzu a wannan kasa ta Nijeriya. kome yana nema ya fi karfin talaka kama daga kan kudin abinci, kudin mota, kudin makaranta, magani da sauran dawainiyar rayuwa. Wallahi ko a mulkin janar Abacha da Maradona ba mu shiga tasku irin wannan ba. Shugaba Buhari sai ya yi da gaske ya dauki mataki a kan miyagum ’yan siyasa da azzaluman ’yan kasuwar da suke maida hannun agogo baya a Nijeriya, Allah ya kawo mana sauki, Amin.
Daga: Ashiru Master Gashua Jihar Yobe.
Jaje ga Dauda Rarara.
Assalamu alaikum Edita. ku isar min sakon jajan ta wata ga shahararren mawakin siyasa, watan Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara. Akan garkuwa da wosu ’yan ta’adda suka yi da shi, har ya ba da kudin fansa Naira million ukku. Allah ya kara tsaremu na kai kuma ya doraka ga makiyanka amin. Daga Tukur M. Sani Kwasara karamar Hukuma Bagudo, Jihar Kebbi 08086408131.
Kira ga Gwamnan Gombe
Kira ga Gwamnan talakawa Talban Gombe. Don Allah ya taimaka da hanya da ta tashi daga Bore ta yi billiri zuwa Ayaba a yi kokari. Domin damina tana zuwa. Allah ya taimaki Gwamna amin. Daga Mista Molta Dikau Tal Maiduguri 07038655371.
Rigimar shugabanni a Kano
Rigimar Kwankwaso da Ganduje, munafunci dodo ne yakan ci mai shi. Allah ya kara wa Barno dawaki. Daga Tukur Maraya Shanono.07032442923.