’Yan majalisa na kawo cikas ga shirin canji na Buhari
Cibiyar Bayar da Shawara ga Jam’iyyu ta zargi ’yan majalisa ga yin cikas ga shirin canji na gwamnatin shugaba Buhari. Cibiyar IPAC, wacce ita ce inuwar gamaiyar dukkanin jam’iyyu da suka yi rajista a kasa ta ce take-taken wasu ’yan majalisa ya zame wani shinge da ya hana samun bunkasar tattalin arzikin kasa. A sanarwar […]

Cibiyar Bayar da Shawara ga Jam’iyyu ta zargi ’yan majalisa ga yin cikas ga shirin canji na gwamnatin shugaba Buhari.
Cibiyar IPAC, wacce ita ce inuwar gamaiyar dukkanin jam’iyyu da suka yi rajista a kasa ta ce take-taken wasu ’yan majalisa ya zame wani shinge da ya hana samun bunkasar tattalin arzikin kasa.
A sanarwar da shugaban IPAC ya sanya wa hannu jiya a Abuja wanda har ila yau shi ne Shugaban Jam’iyyar Accord, Alhaji Mohammed Nalado ya ce kuskure ne wasu ’yan majalisa su yi kiran a binciki Buhari saboda kudin tallafin da ya baiwa gwamnoni ba tare da neman amincewar majalisa ba.