’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike
Suna barazanar bincike da kuma watsi da kasafin duk shugaban jami’an da ya ƙi ba su cin hanci a wurin kare kasafin kuɗin makarantar
Ana zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ɓullo da sabon salon cin hanci inda suke tatsar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi na tarayya.
Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ’yan majalisar suna barazana ga kowane shugaban jami’a ya ba su cin hancin Naira miliyan takwas kafin sun amince da kasafin makarantarsa na shekarar 2025.
Binciken ya gano cewa kwamitin manyan makarantu da na Asusun Tallafin Manyan Makarantu (TETFUND) a Majalisar Wakilai da ta Dattawa sun buƙaci kuɗaɗen ne daga shugabannin manyan makarantun kafin su amince da kasafinsu na 2025.
’Yan majalisar sun nemi kowanne daga cikin shugaban Jami’o’in Tarayya 60 da ke ƙasar nan ya ba su Naira miliyan huɗu ga kwamitin majalisar dattawa da kuma Naira huɗu ga kwamitin majalisar wakilai kafin su amince da kasafin makarantarsa.
- Boko Haram ta kashe sojoji 22 da mayaƙan JTF a Borno
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet
’Yan majalisar na sa ran samun cin hancin jimillar Naira miliyan 480 daga wannan tsari. An kuma gano cewa sun sanya shuagabannin jami’o’i biyu daga yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma su tsara karɓar kuɗaɗen domin kauce wa tonon asiri.
Sun kuma yi barazanar ɗaukar mataki kan masu kunnen kashi a cikin shugabannin jami’an.
A halin yanzu kwamitocin majalisar dokoki ta kasa na bibiyar kasafin hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati domin kare abin da suka gabatar a kasafin shekarar 2025 wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa babban zauren Majalisar a watan Oktoban 2024.
An jima dai ana zargin ’yan majalisa da neman na-goro da kuma cushe a kasafin kuɗi, inda suke barazanar bincike ga waɗanda suke ƙi su taka rawarsu.
Babu rufa-rufa
Shugabannin jami’o da suka bayyana a gaban kwamitocin domin kare kasafinsu sun zargi mambobin kwamitin da neman na-goro kafin su amince da kasafin.
Wasu daga cikin shugabannin jami’o’in da suka nuna turjiya kuma ana musu barazana da bincike ko ƙin amincewa da kasafin makarantunsu.
Bincike ya gano cewa shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai, Honorabul Hassan Fulata daga Jihar Jigawa ya ƙaddamar da karɓar na-goron ne daga ranar 16 ga watan Janairu a yayin wani zama da aka yi da wasu daga cikin shugabannin jami’o’in, inda aka gaya musu ƙarara abin da ake buƙata daga gare su.
Da farko an shirya fara zaman ne da misalin ƙarfe 10 na safe a,ma aka ɗage shi zuwa 3 na yamma saboda wasu shirye-shiryen bayan fage. Ɗaya daga cikin shugabannin jami’o’in da suka halarci zaman ya ce ’yan majalisar ba su yi wata rufa-rufa ba wajen bayyana abin da suke so.
Shugaban jami’ar wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda gudun zagon ƙasa, ya ce ’yan majalisar sun soke su saboda ƙin ba da haɗin kai kamar yadda sauran shugabannin manyan makarantu suka yi ba tare da wata turjiya ba. Ya ce da ta kai ’yan majalisar na musu barazana.
Wasu majiyoyi da suka halarci zaman sun ce mambobin kwamitin sun rika yi wa shugabannin jami’o’in shaguɓe, “da barazanar bincike idan ba mu yi musu abin da suke so ba,” kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Ya bayyana cewa yawancin hukumomi da cibiyoyin gwamnati na guna-guni kan wannan lamari kamar yadda shugabanni jami’o’i ke yi.
Yawancin shugabannin jami’o’i na kokawa bisa yadda ’yan majalisar ke yawan tatsar su kuɗaɗe, lamarin da yanzu ya ɗauki sabon salo saboda barazanar da ’yan majalisar ke musu da sunan bincike.
Wani shugaban jami’a ya bayyana damuwa game da yiwuwar a tura hukumar ICPC ta bincike su, kamar yadda aka yi a baya lokacin da binciken Premium Times ya bankaɗo irin wannan lamari na neman na-goro daga ’yan majalisar dokoki ta ƙasa.
A 2023 Premium Times ta bankaɗo yadda kwamitin manyan makarantu na majalisar wakilai ya ɓullo da salon tatsar kuɗaɗe daga jami’o’i da kwalejojin ilimi da kwalejojin kimiyya da ƙere-ƙere.
Rahoton ya fallasa yadda ’yan majalisar suka riƙa amfani da kamfanonin canjin kuɗaɗe domin karɓar kuɗaɗen haramun ɗin.
A ƙarshe badaƙalar ta kai ga bincike daga hukumar Yaƙi da Ci. Hanci (ICPC) amma kamar an shuka dusa.
Babu abin ICPC za ta yi?
Da yake magana game da ICPC, daya daga cikin ’yan majalisar ya sanae a wurin taron cewa, “Daga ICPC zuwa Shugaban ’Yan Sanda babu wanda ba ya bayyana a gabanmu domin kare kasafin kuɗinsu.”
Premium Times ta tuntuɓi kakakin ICPC, Demola Bakare, ta waya gane da batun ɗan Majalisar na cewa to hukumar taba ba da kai bori ya hau. Amma ya yi dariya sannan ya yi watsi da zargin cewa hukumar na ba da cin hanci ga wani kwamiti.
“Har kun ban dariya, a wurinku na fara jin wannan maganar, amma zan bincika in ji” a cewar Mista Bakare wanda ya yi alƙawarin bayyana matsayin hukumar a gwamnatance daga bisani, amma bai yi hakan ba.
Ɓatar da sawu
Binciken ya gano cewa ’yan kwamitin sun wakilta wani jami’insu ya kula da tura kuɗaɗen ta asusan banki da yawa ta yadda ba za a iya bibiyar su ba. Wannan dabara da sa binciken Premium Times bai iya gano tafiyar kuɗaɗen ba, ko shin shugabannin jami’o’i sun ba da kai bori ya hau.
Binciken ya gano cewa amfani da asusun ajiya da yawa da ba kai tsaye ba da kuma wakilai na rage yiwuwar tura kuɗi zuwa wani asusun ajiya.
Turjiya
Da alama dai a wannan karon shugabannin jami’o’i da dama ba su da niyyar bin wannan umarni, inda suke nuna damuwa bisa yadda ’yan majalisa ke yawan tatsar kuɗaɗe daga hannunsu.
A lokuta da dama shugabannin manyan makarantun kan bayyana a gaban kwamitoci daban-daban na wucin gadi da an dindindin na Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa kan dalillai daban-daban.
A ranar Laraba suka yi irin wannan zama da kwamitin majalisar dattawa amma tattaunawar ba ta yi zafi kamar na Majalisar Wakilai ba.
Ana iya tuna cewa a bara Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ’yan majalisar sun nemi cin hancin Naira miliyan biyar daga kowane shugaban jami’a kafin su amince da kasafin makarantarsa.
Da alama ƙarin kuɗin zuwa miliyan takwas a bana ya ƙara musu damuwa.
Bi-ta-da-ƙulli
Da alama ’yan majalisar sun mayar da Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Farfesa Mu’azu Gusau, hadafinsu, inda yayin zaman nasu ma ranar 16 ga Janairu suka bayyana cewa za su “koya masa darasi saboda taurin kansa.”
Mahalarta taron sun bayyana cewa ’yan majalisar sun soki Farfesa Gusau saboda ya ki ba su haɗin kai kamar sauran shugabannin jami’o’i.
“Ba a san takamaiman abin ya yi musu ba da suka kafa masa ƙahon zuƙa, amma da alama ya ƙi amincewa ne da buƙatarsu ne.
“Wataƙila a baya ma ya yi watsi da buƙatarau, saboda su a kodayaushe kuɗi suke nema,” in ji majiyar da ta nemi a ɓoye sunanta.
’Yan majalisar ba su bayyana yadda za su ɗauki mataki a kansa ba, amma suna da tarihin amfani da barazana da kuma bincike domin tanƙwara mutane su yi yadda suke so.
Cinikin na-goro
A lokuta da dama da ake zargi kwamitoci sun shirya bincike da nufin tozarta wasu mutane, a dabarar su ta tursasa cibiyoyin gwamnati su taka rawar kiɗansu.
Zaman sirri na daga cikin dabarun da suke amfani da su domin tattaunawa da tursasa wa cibiyoyi sa hukumomin gwamnati kan cin hancin da za su ba su.
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Manyan Makarantu na da tarihin hana ’yan jarida halartar zaman su, wanda hakan ke ba da damar yin ƙumbiya-ƙumbiya.
An nemi jin ta bakin Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya kan Ilimin Jama’a, Honorabul Hassan Fulata, domin jin martaninsa, amma har zuwa lokacin da aka kammala wannan labarin bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba.