’Yan majalisa sun sha alwashin sake mika kudurin zabe ga Buhari
Bayan da shugaban kasa ya ki sanya hannu a kudurin dokar zabe , ’yan majalisar dokoki sun yanke shawarar su sake yin aikin a kan kudurin dokar zabe sannan su sake aikewa shugaba Muhammadu Buhari don ya sanya hannu. Shugaban Kasa ya ki sanya hannu a kudurin dokar da majalisar ta aika masa a […]

Bayan da shugaban kasa ya ki sanya hannu a kudurin dokar zabe , ’yan majalisar dokoki sun yanke shawarar su sake yin aikin a kan kudurin dokar zabe sannan su sake aikewa shugaba Muhammadu Buhari don ya sanya hannu.
Shugaban Kasa ya ki sanya hannu a kudurin dokar da majalisar ta aika masa a watan da ya gabata wanda ya canja lokutan zaben kasar.
’Yan majalisar sun sanya zabansu a farko sannan na gwamnoni da na ’yan majalisar jihohi ya biyo baya sai kuma na shugaban kasa a karshe.
Shugaban kasar ya ki sanya hannu a kan kudurin dokar saboda dalilai uku na kundun dokokin kasa.