’Yan majalisa sun soki Abaribe kan karbar belin Kanu

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa ’yan majalisar dattawa daga Kudu maso gabas sun sha suka daga abokanen aikinsu dangane da goyon bayan kungiyar IPOB da ke rajin kafa kasar Biyafara. Zarge-zargen dai sun yi kamari ne yayin taron da majalisar ta gudanar bayan da majalisar ta dawo daga hutun shekara. A […]

’Yan majalisa sun soki Abaribe kan karbar belin Kanu

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa ’yan majalisar dattawa daga Kudu maso gabas sun sha suka daga abokanen aikinsu dangane da goyon bayan kungiyar IPOB da ke rajin kafa kasar Biyafara.
Zarge-zargen dai sun yi kamari ne yayin taron da majalisar ta gudanar bayan da majalisar ta dawo daga hutun shekara.
A karshen taron an dora alhakin lamarin a kan shugaban kungiyar Sanatoci na Kudu maso gabas, Sanata Enyinnaya Abaribe dan jam’iyyar PDP daga jihar Abia musamman tsayawar da ya yi aka bayar da belin shugaban kungiyar IPOB  din.