’Yan majalisa sun tabbatar da dakatar da shugaban hukumar hannun jari

Majalisar wakilai ta kasa jiya ta ce dakatarwar da aka yi wa tsohon darakta janar na hukumar hada-hadar hannun jari, Mounir Gwarzo tana nan daram.   Majalisar yayin da take amincewa da rahoton kwamiti kan kasuwar hannu jari da ma’aikatun hada-hadar hanun jari, Dan majalisa Tajuddeen Ayo Yusuf dan jam’iyyar PDP daga jihar Kogi ya […]

’Yan majalisa sun tabbatar da dakatar da shugaban hukumar hannun jari

Majalisar wakilai ta kasa jiya ta ce dakatarwar da aka yi wa tsohon darakta janar na hukumar hada-hadar hannun jari, Mounir Gwarzo tana nan daram.
 
Majalisar yayin da take amincewa da rahoton kwamiti kan kasuwar hannu jari da ma’aikatun hada-hadar hanun jari, Dan majalisa Tajuddeen Ayo Yusuf dan jam’iyyar PDP daga jihar Kogi ya ce Gwarzo yana da tuhuma da ya kamata ya amsa kuma Ministan Kudi, Kemi Adeosun ta yi daidai da ta dakatar da shi.
 
Sakamakon korafe-korafen da masu ruwa da tsaki suka gabatar, majalisar ta ce hakan ya sanya kwamitin ya gabatar da bincike kan lamfanin mai na Oando.
 
Kuma ’yan majalisar sun ce ya zama wajibi a dawo da ma’aikata biyu na hukumar hada-hadar hanun jari, Misis Anastacia Braimoh da Nazif Abdulsalam bakin aiki cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.
Majaisar ta ce ya zama wajibi ya zama an dawo da ma’aikatan bakin aiki kamar yadda dokar aikin hukumar hada-hadar hannun jari ta tanada.


A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya