’Yan majalisa sun yi abin da bai dace ba – Kerry
Sakataren Harkokin Wajen kasar Amurka John Kerry ya soki ’yan majalisar dokikin kasar bisa ga wasikar da suka rubuta wa kasar Iran, kwanakin baya. Sakatare Kerry ya ce: “Babu dalilin da wasu ’yan majilisar Dattijai guda 47 za su rubuta wa kasar Iran wasika ba akan yarjejeniyar da kasar Amurka ta yi da kasar game […]
Sakataren Harkokin Wajen kasar Amurka John Kerry ya soki ’yan majalisar dokikin kasar bisa ga wasikar da suka rubuta wa kasar Iran, kwanakin baya.
Sakatare Kerry ya ce: “Babu dalilin da wasu ’yan majilisar Dattijai guda 47 za su rubuta wa kasar Iran wasika ba akan yarjejeniyar da kasar Amurka ta yi da kasar game da batun makamin Nukliya ba. Yin haka ya tozarta manufofin kasar Amurka da kasashen ketare kuma ya karya tsohon tarihin kasar .
Ya kara da cewa “yarjejeniyar da Amurka ta kulla game da batun Nukliyar da kasar Iran ba na har abada ba ne domin wani shugaban kasa zai iya rusa ta muddin ya ga cewa ba ta daidai da nasa tsarin ba, amma ba su da hujjar rubuta wa kasar Iran wasika kan wannan batun. Majalisa ba ta da ikon rushe ko wane irin yarjejeniya da shugaban kasa ya kulla da wata kasa, sai dai ko idan ba kasa ba ce kungiya ce don haka wannan abu da wadannan ’yan majilisar suka yi sun yi shishigi kuma sun wuce makadi da rawa.