‘Yan majalisa sun zargi Gwamnan Neja da jan kafa kan kwato dukiyar da aka sace

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta zargi Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello da jan  kafa wurin fara gudanar da cikakken bincike kan mutanen da suka yi watanda da dukiyar  al’ummar jihar musamman a shekara takwas na gwamnatin da ta gabata.’Yan majalisar da suka hada da Mataimakin Shugabanta Alhaji Hussaini Ibrahim daga Mazabar Agaye da Maliki […]

‘Yan majalisa sun zargi Gwamnan Neja da jan kafa kan kwato dukiyar da aka sace
‘Yan majalisa sun zargi Gwamnan Neja da jan kafa kan kwato dukiyar da aka sace

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta zargi Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello da jan  kafa wurin fara gudanar da cikakken bincike kan mutanen da suka yi watanda da dukiyar  al’ummar jihar musamman a shekara takwas na gwamnatin da ta gabata.
’Yan majalisar da suka hada da Mataimakin Shugabanta Alhaji Hussaini Ibrahim daga Mazabar Agaye da Maliki Madaki daga Mazabar Bosso suna daga cikin wadanda suka zargi Gwamnan kan yadda yake neman barin wannan badakalar ta sha ruwa duk da alkawarin da ya yi wa ’yan majalisar yayin da ya  gabatar da kasafin kudi bana cewazai bin kadin duk kudin da aka batar da sawunsu ta kowace fuska.
’Yan majalisar sun nanata matsayinsu na tabbatar da cewa Gwamnan ya bi kadin kudin  da aka karkatar da su ta hanyoyin yaudara suka fada aljifan wasu kalilan din mutane.
Maliki Madaki ya ce, “Ba yadda za a yi mu sa ido wasu mutane kalilan su cinye dukiyar jama’ar jihar ba, musamman ma’aikata da suka shafe shekaru suna bauta wa jihar amma su rasa tudun dafawa bayan sun ajiye aiki.”
Da yake jawabi kan lamarin Kwamishinan Kudi Malam Ibrahim Balarabe ya shaida wa majalisar cewa gwamnatin tana ci gaba da daukar matakan da suka kamata kamar yadda doka ta tanada game da lamarin kwato dukiyar da aka sace a jihar.
Malam Ibrahim Balarabe ya ce, kwato dukiyar jama’a da aka wawure na daya daga cikin alkawuran da Gwamna Abubakar Sani Bello ya dauka domin tabbatar da canji a rayuwar jama’a. kuma da zarar an gama hada  duk hujjojin da suka kamata, za a dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace.