…’Yan majalisa za su maka mukarrabin Kwankwaso a kotu

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun ce  za su gurfanar da tsohon mai taimaka wa tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a bangaren Watsa Labarai Sharu Garba Gwammaja kan zargisan da yi musu kazafin sun karbi Naira miliyan 17 kowannensu daga Gwmana Abdullahi Umar Ganduje don su zame masa ’yan amshin shata kan rigimar da ta […]

…’Yan majalisa za su maka mukarrabin Kwankwaso a kotu
…’Yan majalisa za su maka mukarrabin Kwankwaso a kotu

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun ce  za su gurfanar da tsohon mai taimaka wa tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso a bangaren Watsa Labarai Sharu Garba Gwammaja kan zargisan da yi musu kazafin sun karbi Naira miliyan 17 kowannensu daga Gwmana Abdullahi Umar Ganduje don su zame masa ’yan amshin shata kan rigimar da ta kunno kai tsakaninsa da Kwankwaso.
Sharu Garba Umar Gwammaja ya shiga kafafen watsa labarai ne ya bayyana cewa ’yan majalisar sun aikata abin kunya na karbar cin hanci daga Gwamna Ganduje, kalaman da ba su yi wa ’yan  majalisar dadi ba, suka hadai kai don daukar matakin shari’a a kansa.
Shugaban Masu Rinjaye na Majlisar, Abdullahi Yusuf Ata daga mazabar Fagge ne ya yi magana a madadin ’yan majalisar, inda ya ce dole ne majalisar ta bi hakkinta kan wannan kazafi da ak yi mata, kuma ya ce tuni suka mika kokensu ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano don daukar mataki na gaba.  “Mun mika
batun kazafin da Sharu Garba Gwammaja ya yi mana ga ’yan sanda don daukar mataki na gaba. A yanzu haka ’yan sandan sun tabbatar mana cewa Sharu yana hannunsu,” inji shi.
Alhaji Yusuf Ata ya ce wajibi ne majalisar ta dauki matakin shari’a matukar Sharu Gwammaja ya gaza bayyana hujjojin da za su tabbatar da da’awarsa cewa sun karbi makudan kudi daga Gwamna Ganduje a matsayin toshiyar baki.