’Yan majalisar Amurka na wasa da wuta –Sakataren Baitul-malli
Sakataren Baitul malin Amurka, Jack Lew, ya gargadi ‘yan majalisar kasar kan cewa “suna wasa da wuta,” a daidai lokacin da ’yan jam’iyyar Republican suka yi barazanar kin daidaitawa da Shugaba Obama kan kudin da za a kashe na shirin kula da lafiya, ko da za ta kai ga an gindaya wa kasar iyakar ciwo […]
Sakataren Baitul malin Amurka, Jack Lew, ya gargadi ‘yan majalisar kasar kan cewa “suna wasa da wuta,” a daidai lokacin da ’yan jam’iyyar Republican suka yi barazanar kin daidaitawa da Shugaba Obama kan kudin da za a kashe na shirin kula da lafiya, ko da za ta kai ga an gindaya wa kasar iyakar ciwo bashi.
Shugaba Barack Obama ya ja kunnen ’yan jam’iyyar Republican da ke majalisa da su daina yin barazana wajen amincewa da kasafin kudi, don shawo kan tsayar al’amura da harkokin mulki a kasar.
“Da zarar ’yan majalisa sun kada kuri’ar ci gaba da harkokin gwamnati, to sai kuma su kada kuri’ar amincewa da daga kimar ciwo bashi, ta yadda za mu iya biyan bukatunmu,” inji shi.
Shi kuwa Shugaban Majalisar Wakilai ta Amurka, John Boehner ya bayyana cewa ’yan Republican masu rinjaye ba za su amince a kara wa Amurka damar ciwo bashi ba, har sai fadar White House ta yi sassuaci a bukatarta, inda yake bayyana ra’ayinsa game da tsayawar harkokin mulki da ayyukan hukuma a Amurka.
“Ba za mu bayar da izinin karin damar ciwo bashi ba,” a cewar Boehner, a wata hirar da gidan talabijin na ABC ya yi da shi.
“Na gaya wa shugaban kasa, cewa babu gudu ba ja da baya. Ba za a samu kri’un da za a kada har su bayar da damar sabon tsarin ciwo ba shi. Kuma shugaban kasa na cikin hadarin kasa biyan bashi, matukar bai tattauna da mu ba,” inji shi.
Lew ya ce Amurka za ta rasa damar rancen kudi nan da rnar 17 ga watan Oktoban bana, kuma kudin da ke hannunta duka Dala biliyan 30 ne, wadanda ba za su iya biyan bukatar da kimarta ta kai Dala biliyan 60 ba. Don haka lokacin na iya kurewa.
“Ina mai tabbatar muku nan da rnar 17 ga Oktoba mun kure damarmu ta rancen kudi, kuma ’yan majalisa na wasa da wuta,” kamar yadda ya bayyana wa tashar talabijin ta CNN. “Idan ba su kara yawan bashin ba, muna da kurerren lokaci, kafin mu iya samar da mafita,” inji shi.
Bashin da ake bin kasar Amurka ya kai Dala Tiriliyan 16 da biliyan 700. Kuma jam’iyyun kasar, sun kasa cimma matsaya a majalisa wajen samar da karin kudi don aiwatar da sabon tsarin kula da lafiya na Obama, wanda a Turance aka yi wa lakabi da “Obamacare.”