‘Yan majalisar APC na yunkurin tsige Gwamnan Akwa Ibom

Rahotanni na bayyana cewa, ‘yan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom wanda suka koma jam’iyyar APC kuma  aka kore su, na shirin tsige Gwamnan jihar Udom Emmanuel. A yau ne lokacin da Gwamnan jihar ya ziyarci majalisar dokokin jihar kuma korarrun ‘yan majalisa suke yunkurin mamaye zauren majalisar da nufin su suka fi rinjaye a zauren. […]

‘Yan majalisar APC na yunkurin tsige Gwamnan Akwa Ibom

Rahotanni na bayyana cewa, ‘yan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom wanda suka koma jam’iyyar APC kuma  aka kore su, na shirin tsige Gwamnan jihar Udom Emmanuel.

A yau ne lokacin da Gwamnan jihar ya ziyarci majalisar dokokin jihar kuma korarrun ‘yan majalisa suke yunkurin mamaye zauren majalisar da nufin su suka fi rinjaye a zauren.

Rikici ya kaure lokacin da jami’an tsaron suka nemi su dakatar da Kakakin majalisa jihar Nse Ntuen wanda ake son tsige wa da sauran ‘yan majalisar hudu daga shiga zauren majalisar.