’Yan majalisar Filato da kotu ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki

’Yan Majalisar Dojojin Jihar Filato wadanda kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu sun lashi dowawa bakin aiki.

’Yan majalisar Filato da kotu ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki

Gwamman Jihar Fiato, Caleb Mutfwang

’Yan Majalisar Dojojin Jihar Filato wadanda kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu sun lashi dowawa bakin aiki.

A ranar Litinin ’yan jam’iyyar PDP 16 da kotun daukaka kara ta kwace kujerun nasu suka lashi takobin ci gaba da aiki daga ranar Talata.

Kotun daukaka kara ta kwace kujerunsu ne a bisa hujjar cewa jam’iyyarsu ba da ta da halastaccen shugabanci da zai tsayar da ’yan takara a zaben 2023.

Amma da suke jawabi ga manema labarai a Jos ranar Litinin , wakilinsu, Ishaku Maren, ya ce hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na jami’yyar ya nuna cewa su ne halastattun ’yan majalisar.

Don haka suka ce za su dawo majalisar a ranar Talata da majalisar za ta dawo daga hutun wata biyu da ta je.

An dawo da wutar lantarki a Kaduna

An kashe ɗan banga da yin garkuwa da ’yan mata 6 a Neja

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace