Yan Majalisar Katsina ba za su zama ’yan amshin shata ba – Shugaban Masu Rinjaye
Alhaji Lawal Isa Kuraye shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Katsina kuma yana wakiltar karamar Hukumar Charanchi ne, a zantawarsa da Aminiya ya ce ’yan majalisar ba su zama ’yan amshin shata ba duk da cewa dukkansu jam’iyyarsu daya da Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari: Aminiya: Jam’iyyarku ta APC ta yi kaka-gida […]
Alhaji Lawal Isa Kuraye shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Katsina kuma yana wakiltar karamar Hukumar Charanchi ne, a zantawarsa da Aminiya ya ce ’yan majalisar ba su zama ’yan amshin shata ba duk da cewa dukkansu jam’iyyarsu daya da Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari:
Aminiya: Jam’iyyarku ta APC ta yi kaka-gida a Majalisar Dokokin Jihar Katsina, me za ka ce dangane da gwamnatin Alhaji Aminu Masari?
Lawal Kuraye: Koda yake kamar Hausa ka yi da ka ce kaka-gida, Allah ne Ya ba mu nasara Ya kuma sa jama’ar Jihar Katsina suka zabe mu baki daya. Kuma tun daga wannan lokaci mutanen jihar a siyasar da ake yi a Najeriya sun yi abin da ba a taba yin sa ba, domin tun daga dan majalisar jiha zuwa sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da Gwamna duk ’yan jam’iyarmu ne. Sai kuma Allah Ya rufe mana da Shugaban kasa shi ma dan jam’iyyarmu, ka ga ke nan a tarihin Najeriya a kuma Jihar Katsina ba a taba yin irin haka ba. Wannan ya kuma sanya shi Gwamna Aminu Bello Matsari a yadda muka taho mutanen Jihar Katsina sun fara ji kuma sun fara gani da yardar Allah. Kuma insha Allahu da irin matakan da suka dauka abin zai zama Allah sam barka. Haka kuma a yayin da ya kammala kafa gwamnatinsa cikakkiya za a yaba. Mu kuwa a matsayinmu na ’yan majalisa kasancewar mu 34 jam’iyarmu daya ina sanar da mutanen Katsina cewa za mu yi bakin kokarinmu wajen ganin mun hada kai domin gwamnatin ta ci gaba ba tare da mun sadaukar da wani hakki namu ba, domin Jihar Katsina ta ci gaba. Wannan ba zai hana a samu dan sabanin ra’ayi nan da can ba. Wannan ba zai hana mu ba da hadin kai ba inda ya kamata mu ba da, inda kuma ya kamata mu jajirce a matsayinmu na ’yan majalisa za mu yi, in Allah Ya yarda.
Aminiya: Wasu na ganin kuna iya zama ’yan amshin shatan bangaren zartarwa kasancewar dukkanku jam’iyyarku daya, me za ka ce?
Lawal Kuraye: Mene ne ’yan amshin shata, ai idan shata ya fadi daidai su ma ’yan amshinsa sai su fadi daidai. Idan gwamnati ta zo da abin da yake da kyau sai mu ce a yi. Mu ma idan muka fito da abin kirki ai dole sai a yi. In Allah Ya yarda Alhaji Aminu Bello Masari a matsayinsa na tsohon dan Majalisar Tarayya na tabbatar ya san ’yanci da hakkin ’yan majalisa ba zai yi abin da zai hana mu aikinmu ba, kuma ba zai saba mana ba.Ina jin a jihohin Najeriya jihohi uku ne aka samu irin haka, wato Jihar Katsina da Sakkwato inda tsohon shugaban majalisa ya zama Gwamna a wasu wuraren kuwa ’yan majalisa ne. Wannan ya sa nake ganin gwamnatinsa ba za ta yi wani abu da ba daidai ba ga ’yan majalisa, domin shi ma ya taba zama dan majalisa har ya shugabance ta. Saboda haka ba na jin zai yi abin da zai kai ga abin da kuke kira ’yan amshin shata. Amma kuma barin in yi muku gyara ku ’yan jarida ai Shata idan ya fadi magana ai dai-dai yake fadi sai wakar ta yi dadi, in da ’yan amshinsa na fadin ba daidai ba ne ai wakar ba za ta yi dadi ba.
Aminiya: Me za ka ce game da mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari?
Lawal Kuraye: Abin da kawai zan ce da ’yan Najeriya shi ne mu kara gode wa Allah, domin Ya fidda mu daga kangin da muke ciki a ’yan shekarun baya. Shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na tsohon Janar na soja da ya yi mulkin kasar nan yana bin al’amura ne sannu a hankali tare da neman warware zare da abawa. Na yi imani nan da ’yan watanni ’yan Najeriya za su ga canji mai ma’ana kai an ma fara gani. Wasu na cewa wai mulkinsa na tafiyar hawainiya amma a matsayina na Musulmi, gaggawa daga aikin Shaidan yake. Saboda haka komai a bi shi a hankali shi ne daidai. Saboda haka ba na jin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na tafiyar hawainiya.
Bari in mayar da hankalin ’yan Najeriya baya ga wani mawaki wanda ya ce ’yan Najeriya su gode wa Allah Buhari ne ke mulki amma sai ya ambaci wasu al’amura da ke damun kasar ciki har da rashin tsaro da cin hanci da rashawa da rashin ilimi da sauransu. Wadanda gyara su sai a hankali idan kuwa ka ce za ka yi gaggawa, za ka yi wani abu da ake cewa kara da kiyashi. Mu kuma ba mu son Shugaba Buhari ya yi kara da kiyashi.
Aminiya: Wane tabbaci za ka ba wa mazabarka na ba su wakilci mai kyau a majalisa?
Lawal Kuraye: Ina ganin al’ummar Charanchi sai su gode wa Allah, saboda a yayin da muka je majalisa da aka zo yin zaben shugabanni sai Allah Ya ba mu shugabancin masu rinjaye a majalisa, wannan kawai ya nuna cewa akwai wani abu da abokan aikina suka gani a tare da ni har suka zabe ni Shugaban Masu Rinjaye. Baya ga wannan gwargwadon ’yar sanayyata domin na yi Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Chanranchi sau biyu, na kuma kasance daya daga cikin masu taimaka wa wani dan majalisa a Abuja wanda ya sauka kwanan nan. Da wannan dan sanin makaman aiki da na samu na dan cikin cokali da kuma goyon bayan abokan aikinmu a majalisa zan tabbatar da duk wani kudiri da zai kawo ci gaban karamar Hukumar Charanchi za su ba mu goyon baya tun da ga shi sun ba mu goyon baya inda suka zabe mu Shugaban Masu Rinjaye. Haka idan aka kawo kudiri na ci gaban sauran kananan hukumomi ni ma zan ba su goyon baya, tunda abin ba-ni-gishiri ne in-ba-ka manda. Saboda haka in Allah Ya yarda duk wani abu da zai kawo ci gaba ga karamar Hukumar Chiranci za mu ga mun yi shi cikin ikon Allah.