’Yan Majalisar Sakkwato 27 daga cikin 30 sun koma APC
Yan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato 27 daga cikin 30 sun fice daga Jam’iyyar PDP inda suka koma Jam’iyyar APC a shekaranjiya Laraba.Shugabana Kwamitin Watsa Labarai na Majalisar Malami Basakkwace, ya shaida wa jaridar Premium Times ta wayar tarho cewa wakilan majalisar sun yanke shawarar hake ne domin bi sawun Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako […]

Yan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato 27 daga cikin 30 sun fice daga Jam’iyyar PDP inda suka koma Jam’iyyar APC a shekaranjiya Laraba.
Shugabana Kwamitin Watsa Labarai na Majalisar Malami Basakkwace, ya shaida wa jaridar Premium Times ta wayar tarho cewa wakilan majalisar sun yanke shawarar hake ne domin bi sawun Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako daya daga cikin gwamnonin PDP biyar da suka koma APC.
“Mun koma ne sakamakon shawarar da Gwamna Aliyu Wamakko ya yin a komawa APC,” inji shi.
Wadanda suka koma APC din sun hada da shugabana majalisar da manyan jami’an majalisar.
Malami Basakkwace ya ce tun lokacin da gwamnonin suka koma APC, mutane daga mazabu 27 suke matsa wa ’yan majalisar su bi sawun Gwamnan. Ya ce rikicin da PDP ke fama da shi, wanda ya jawo rarrabuwar jam’iyyar a matakin jiha da kasa ya taimaka wajen ficewarsu daga cikinta.
Wani dan majalisar, Abdulsamad Dasuki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sarin mulkin Najeriya ya ba su ’yancin shiga kungiya ko jam’iyya kuma rikicin da ke cikin PDP yana dada karuwa ne a kullum.
“Lemar PDP ta kekkece, don haka wajibi ne mu bi bukatar jama’armu,” inji ta. Ya ce, sauran mambobi uku ma za su koma APC, “Ina da tabbacin za su sahu idan suka dawo, ba su nan ne a yau (Laraba) sakamakon rashin lafiya da sauran hidimomi,” inji shi.