’Yan Majalisar Tarayya 5 sun sauya sheƙa zuwa APC
’Yan Majalisar Wakilai guda biyar daga manyan jam’iyyun adawa na PDP da LP sun sauya sheka zuwa APC
’Yan Majalisar Wakilai guda biyar daga manyan jam’iyyun adawa na PDP da LP sun sauya sheka zuwa APC.
A zaman majalisar na ranar Alhamis shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar cewa ’yan jam’iyyar LP huɗu da wata ’yar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC.
Daga cikinsu har da ƙananan, ’yar gidan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori.
Mambobin LP da suka koma APC su ne, Donatus Matthew (Kaduna) da Tochukwu Chinedu Okere (Imo) da Akiba Bassey (Cross River) da kuma Esosa Iyawe (Edo).
Masu sauya shekar sun danganta sauya sheƙar tasu da rikicin cikin gida a jam’iyyunsu.