’Yan Majalisar Tarayya 6 daga Jihar Ribas sun koma APC

’Yan Majalisar Jihar Ribas 3 ne kawo yanzu zuka rage ba su sauya sheka zuwa APC ba

’Yan Majalisar Tarayya 6 daga Jihar Ribas sun koma APC

’Yan Majalisar Wakilai 6 daga Jihar Ribas sun sanar da sauya shekarsu daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudden ne ya karanta takardun sauya shekar su a zauren majalisar a ranar Talata.

Masu sauya shekar sun haɗa da Dumnamene Dekor, Cyril Hart Godwin, Solomon Bob, Victor Obuzor, Blessing Amadi da Felix Uche.

’Yan majalisar sun danganta matakin da suka ɗauka da rikicin shugabanci da rabuwar kai a PDP, wanda suka ce ya hana su cimma manufofin siyasa da na wakilci yadda ya kamata.

Lamarin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu ’yan majalisar jihar guda huɗu sun sauya sheka zuwa APC daga PDP da Labour Party (LP), abin da ya ƙara rage ƙarfin jam’iyyun adawa a jihar.

Waɗanda suka sauya sheka a baya daga PDP sun haɗa da Boniface Emerengwa, Awaji-Inombek Abiante da Boma Goodhead, yayin da Manuchim Umezuruike mai wakiltar Fatakwal I ya sauya sheka daga LP.

Dukkansu sun danganta sauya shekar da rikicin shugabanci da rabuwar kai a cikin jam’iyyunsu.

Ana ganin wannan guguwa ta sauya sheka na da nasaba da sabon sauyin siyasa a Jihar Ribas bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya koma APC.

Da wannan sauyin, yanzu Jihar Ribas ta rage da ’yan majalisar wakilai uku kacal da ba su sauya sheka zuwa APC ba.

Su ne Jagoran ’Yan Adawa, Kingsley Chinda, Kelechi Nworgu da Anderson Allison Igbiks, dukkansu na PDP.