’Yan mata da samarin Arewa

  Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan auren mace tagari, ta hanyar guje wa kyale-kyale a tsakanin samari da ’yan matan Arewa. Mace mai hankali da nutsuwa, ‘yar gidan mutunci, mai kyau daidai gwargwado, ita ce ta aure. Amma idan ka biye wa zuciyarka ka dauki kyale-kyalen duniya, to ko ka […]

’Yan mata da samarin Arewa

 

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan auren mace tagari, ta hanyar guje wa kyale-kyale a tsakanin samari da ’yan matan Arewa. Mace mai hankali da nutsuwa, ‘yar gidan mutunci, mai kyau daidai gwargwado, ita ce ta aure. Amma idan ka biye wa zuciyarka ka dauki kyale-kyalen duniya, to ko ka yi auren ma ba za ka samu kwanciyar hankali ba. Ka yi soyayya da yarinya tsawon shekaru hudu ko fiye da haka, a karshe ka aure ta, amma wallahi wata rana idan ta kwaba maka wata maganar idan ba dannar zuciyarka ka yi ba take za ka rabza mata saki uku.

Wani dan lokaci kadan da ya wuce bincike ya nuna a kasashen Yammacin Afirka an fi samun zawarawa a Najeriya, Najeriya din ma a Arewacin kasar. Idan muka yi duban tsanaki rashin kyakkyawan lafazi na daga cikin abin da ke sa a saki matan. Wata idan aka ce ma bazawara ce ko kadan ba za ka taba yarda ba, saboda za ka ganta yarinya ce shakaf (‘yan uwana matasa idan budurwa kuke son aura sai kun kula, domin tsaf za ka auri sauna ga-wawa a matsayin budurwa). Irin wadannan mata kuma idan ka bi diddigi harshensu ne ke sa a  sake su.

An bata ma rai a waje, ka shigo gida ba tarba mai kyau, ka kawo cefane an karba a raine ba godiya, sai dai a nuna ma ka gaza. Kina matar mutum amma ba za ki ba shi hakuri ba. In kin yi masa laifi, to ta ya zamanku zai yi karko? Kina jin cewa ke kyakkyawa ce idan ma ya sake ki kina da masoya da yawa, to kin yi a banza, kina fara zaman zawarcin a gidanku za ki gane shayi ruwa ne…

 Ya Allah Ka azurta mu da mata nagari.

Za a iya tuntubar Kainuwa Hadejia ta: 08100229688/09073801967 Nasiru Kainuwa Hadejia <[email protected]>