’Yan matan Chibok 42 da suka kubuta sun kammala karatu a Filato da Katsina

’Yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram bayan sace su daga Makarantar Sakandaren Chibok ranar 14 ga Afrilun 2014, sun kammala karatunsu a makarantu masu zaman kansu a jihohin Filato da Katsina. ’Yan matan wata kungiyar jinkai mai zaman kanta da ake kira kungiyar Kula da ’Yan mata (GCC) a karkashin […]

’Yan matan Chibok 42 da suka kubuta sun kammala karatu a Filato da Katsina

’Yan matan Chibok da suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram bayan sace su daga Makarantar Sakandaren Chibok ranar 14 ga Afrilun 2014, sun kammala karatunsu a makarantu masu zaman kansu a jihohin Filato da Katsina. ’Yan matan wata kungiyar jinkai mai zaman kanta da ake kira kungiyar Kula da ’Yan mata (GCC) a karkashin jagorancin Dokta Mairo Mandara, wata fitacciyar mai fafutikar ilimantar da  ’yan mata a Najeriya ta dauki nauyinsu tare da hadin gwiwar Gwamnatin  Jihar Barno. ’Yan matan Chibok 42 suna cikin jerin 56 da suka tsira daga hannun ’yan ta’adda bayan sace su a makarantarsu a shekarar 2014.

Lokacin da take jawabi wajen bikin Dokta Mandara ta tunato da kalubalen da ’yan matan Chibok din suka fuskanta bayan ceto su, inda ta ce an rika kyararsu a kokarin da suke yi na  neman wata sabuwar makarantar da za su kammala karatunsu. 

“Yau rana ce ta musamman ga kungiyar GCC saboda wani rukuni na ’yan matanmu an kebe su daga bainar jama’a na tsawon shekara uku. Abu ne mai wahala sama musu makaranta a lokacin da muka dauki alhakin kula da wadannan ’yan mata. Makarantu sun ki karbarsu saboda tsoron abin da zai biyo baya ko ya same su idan aka gano cewa suna makarantar,” inji ta. 

Ta nuna godiyarta ga Gwamnan Jihar Barno, da Gidaunaiyar MalalaYousafzai, wadda ta ce ta yi matukar kokarin ganin cewa ’yan matan Chibok din sun kammala karatunsu na sakandare.