’Yan matan Chibok 57 sun fara karatun digiri a Jami’ar Amurka ta Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyin karatunsu na jami’a bayan Boko Haram ta sako su.

’Yan matan Chibok 57 sun fara karatun digiri a Jami’ar Amurka ta Najeriya

’Yan matan makarantar Chibok 57 da aka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram sun fara karatu a matakin digirin farko a Jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN).

’Yan matan Chibok din sun fara karatun digirinsu na farko wanda Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyi a jami’ar ne bayan kammala karatun sharan fage a jami’ar ta AUN da ke Yola, Jihar Adamawa.

Wasu daga cikin daliban da suka zanta da Aminiya a wurin bikin rantsar da su ranar Litinin, sun bayyana farin cikinsu game da samun damar ci gaba da karatunsu, abin da suka dade suna burin samu bayan Boko Haram ta sako su.

Sanarwar da hukuma jami’ar AUN ta fitar ta hannun kakakinta, Dan Okereke ta ce ’yan matan Chibok 57 na daga cikin sabbin dalibai 57 da aka rantsar a jami’ar.

“Jami’ar Amurka ta Najeriya ta kammala bikin kaddamarwa da karbar rantsuwar sabbin dalibai na wannan shekara, ciki har da daliban makarantar Chibok 57.”

Sanarwar ta ambato Shugaban Jami’ar, Margee Ensign, yana kira ga sabbin daliban da su lalubo mafita ga matsalolin da suka addabi al’umma a cikin gida da matakin duniya.

A cewarsa, matsalolin sun hada hada da talauci, yake-yake, cin zali, danniya, kwararowar hamada, sauyin yanayi, da gurbacewar muhalli da sauransu.

A watan Afrilun 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka yi dirar mikiya a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata da ke garin Chibok a Jihar Borno, inda suka yi awon gaba da daliban da ke shirin rubuta jarabawar kammala sakandare.

Kungiyar ba ta sako su ba sai bayan shekara biyar, bayan nan ne gwamnati ta dauki nauyin karatunsu.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi