’Yan matan Chibok: Ba a yi bikin ranar yara a Borno ba
Ba a gudanar da bukukuwan Ranar Yara da aka saba a Borno ba, saboda nuna bakin ciki da alhinin sace ’yan matan makarantar sakandaren garin Chibok makonni bakwai da suka gabata.Majalisar dinkin Duniya ce ta ware kowace ranar 27 ga Mayu don zama ranar tunawa da yara, inda ’yan makaranta ke gudanar da fareti a […]
Ba a gudanar da bukukuwan Ranar Yara da aka saba a Borno ba, saboda nuna bakin ciki da alhinin sace ’yan matan makarantar sakandaren garin Chibok makonni bakwai da suka gabata.
Majalisar dinkin Duniya ce ta ware kowace ranar 27 ga Mayu don zama ranar tunawa da yara, inda ’yan makaranta ke gudanar da fareti a gaban shugabanni don nuna farin ciki da zagayowar ranar tare da mika korafe-korafensu.
Maimakon haka wasu kungiyoyin sa kai na fararen hula da na ma’aikata da na matasa da na ’yan kasuwa da na likitoci da na iyaye da malamai da sauransu da suka kai 35 ne suka gudanar da jerin gwano don nuna bakin ciki da bacin ransu tare da matsin lamba ga gwamnati ta kara kaimi wajen kubutar da ’yan matan.
kungiyoyin sun yi tattaki daga makarantar Yerwa da ke Gidan Madara zuwa Gidan Gwamnatin Jihar dauke da kwalaye masu cewa: “Ku dawo mana da ’ya’yanmu” da “Muna goyon bayan ilimin ’ya’ya mata” da “Muna son zaman lafiya” da sauransu, sun mika kokensu ga Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Zanna Umar Mustafa.
A jawabin jagoran kungiyoyin, Jakadan Zaman Lafiya a Jihar, Ahmed Shehu, ya ce talakawa suna cikin wahala saboda tabarbarewar tsaro, sai ga shi yanzu kullum sai an kashe mutane, ko a yanka su ko a barnata dukiyarsu ko a kone garinsu, “Don haka muna rokon masu ruwa da tsaki a harkar tsaro su mike tsaye su magance wannan matsalar, wadda ba ta shafi wata jiha ko bangare ko wata kabila ko addini daya ba ne kawai, matsala ce da ta shafi Najeriya,”
Ya bukaci a canja salon tsaro a kasar nan, inda ya ce bai kamata gwamnati ta nade hannu tana kallo matsalar na neman gagara ba, “Duk da cewa mun san gwamnati ta ce tana iya
kokarinta wajen shawo kan wannan matsalar, to, amma dole ne mu mata damuwarmu a kan wannan lamari, don kara mata karfin gwiwa,” inji shi.
Ahmed Shehu ya ce an sace ’yan mata a kananan hukumomin Dikwa da Konduga da Gwoza, sannan a wannan lokaci an sace dalibai mata a Chibok, ya ce akwai bukatar hada
hannu duk da bambancin siysa da addini da kabilanci da bangaranci wajen nuna kyamar garkuwa da yaran, tare da zaburar da gwamnati ta kara kaimi wajen kubutar da su.
Da yake mayar da jawabi Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya nanata kudirin gwamnatin jihar na kokarin gano ’yan matan duk da cewa sha’anin tsaron ba na hannunta ba ne. Ya ce, gwamnatinsu ta damu kwarai da wannan lamari, kuma ya yi alkawarin mika sakonsu zuwa gaba.