’Yan matan Chibok: Ba za mu amince da sharadin Boko Haram ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana tattaunawa da wasu shugabannin kungiyar Boko Haram domin ceto ’yan matan Chibok fiye da 200 da suka sace, sai dai Buhari ya ce ba za su amince da sharuddan da kungiyar ta shimfida ba. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Paris a lokacin da yake amsa […]

’Yan matan Chibok: Ba za mu amince da sharadin Boko Haram ba – Buhari
’Yan matan Chibok: Ba za mu amince da sharadin Boko Haram ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana tattaunawa da wasu shugabannin kungiyar Boko Haram domin ceto ’yan matan Chibok fiye da 200 da suka sace, sai dai Buhari ya ce ba za su amince da sharuddan da kungiyar ta shimfida ba. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Paris a lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan Najeriya mazauna kasar faransa a ranar Talata.
A ranar 14 ga Afrilun bara ne ’yan Boko Haram suka sace ’yan matan a makarantar Sakandaren Chibok, kuma gwamnatin Buhari ta damu da ci gaba da zaman daliban a hannun wadanda suka sace su.
Ya ce lamarin ya jawo hankalin kasashen duniya, inda ya nanata kudirin gwamnatinsa na ganin an sako daliiban. “Batun ’yan matan Chibok ya mamaye zukatanmu, kuma saboda yadda duniya ta zuba mana ido da yadda ake nuna tausaya a sassan kasar da duniya, gwamnati tana tattaunawa da wasu shugabannin Boko Haram,” inji Buhari.Sai dai ya ce, saboda muhimmnacin da batun yake da shi, gwamnatinsa tana kokarin tabbatar da hakikanin ’ya’yan kungiyar don kada ta yi sulhu da mutanen da ba su ba. “Abu ne mai matukar muhimmanci da ya kamata mu gano shin su ne shugabannin Boko Haram na gaskiya? Wannan shi ne na daya. Na biyu mece ce bukatunsu? Bayanan da muka fara samu suna da karfafa gwiwa,” inji shi.
Ya ce daya daga cikin sharuddan da Boko Haram ta gindaya kan sako ’yan matan shi ne a sako wani shugabansu da ke da muhimmanci wajen kera musu bama-bamai. Shugaban kasar ya ce gwamnati ba za ta amince da wannan bukata ba. “Suna son mu sake daya daga cikin shugabanninsu mai muhimmaci wajen kera musu bama-baman da suke haifar da bala’i a kasar nan ta hanyar ruguza coci-coci da masallatai da kasuwanni da tashoshin mota da sauran wurare. Amma yana da matukar muhimmanci idan za mu tattauna da kowa, muna bukatar sanin matsayinsa. Su kawo dukkan ’yan matan tukun, sannan mu shirya batun sulhu. Zan kyale su dawo Najeriya ko a kyale su a cikin jama’a, amma dole mu yi taka-tsantsan.”
Ya kara da cewa: “Damuwarmu kan ’yan matan Chibok ita ce, yaya mutum zai ji a ce yana da ’ya mai shekara 14 zuwa 18 ba a san inda take ban a tsawon shekara daya da rabi. Iyaye da dama sun mutu suna da burin a ce sun ga kaburburan ’ya’yansu maimakon halin da suke ciki a yanzu. Wannan ya jawo damuwa a daukacin duniya, kuma shi ya sa wannan gwamnati take tsaka-mai-wuya kan yadda za ta kwato wadanda suke raye.”
Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa tana yin duk abin da ya wajaba wajen inganta tattalin arziki wajen samar da kayayyakin inganta rayuwa a muhimman sassa.