‘Yan matan Chibok bayan shekara daya: Ba amo ba labari
A ranar Talatar da ta gabata ne aka cika shekara daya da sace ’yan matan makarantar sakandaren Chibok da ake zargin mayakan Boko Haram da sacewa. ’Yan matan na Chibok su 276 da ke karatu a Sakandaren Gwamnati na garin Chibok a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas, sace su ya jawo kungiyoyi na […]
A ranar Talatar da ta gabata ne aka cika shekara daya da sace ’yan matan makarantar sakandaren Chibok da ake zargin mayakan Boko Haram da sacewa. ’Yan matan na Chibok su 276 da ke karatu a Sakandaren Gwamnati na garin Chibok a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas, sace su ya jawo kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya da daidakun jama’a sun yi ta kirarye-kiraye ga shugabanni da mahukuntan kasar nan da ma na kasashen duniya kan su kara himma tare da daukar matakai domin ganin an kubutar da daliban.
A ranar Talatar kungiyoyi da dama karkashin kungiyar nan ta #BringBackOurGirls, sun hada gangami a Abuja babban birnin Tarayya domin kara yin kira ga hukumomi kan su gaggauta kubutar da ’yan matan.
A ranar 14 ga watan Afrilun bara ne mayakan Boko Haram suka auka wa makarantar ’yan mata ta garin Chibok a Jihar Borno suka sace ’yan mata 276 a lokacin da suke shirin rubuta jarrabawa. ’Yan mata 57 daga cikinsu sun tsere amma har yanzu babu wani labari a kan sauran ’yan matan.
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo yana ikirarin cewa ya aurar da ’yan matan tare da musuluntar da wasu daga cikinsu.
kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya ta Amnesty ta ce mayakan Boko Haram suna lalata da wasu daga cikin ’yan matan, tare da tursasa su daukar makamai don fafata yaki.
Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa ta san inda ake garkuwa da ’yan matan na Chibok, amma tana tsoron kada a kashe su wajen kokarinta na kubutar da su.
Batun sace ’yan matan na daya daga cikin dalilan da suka jawo wa gwamnatin Goodluck Jonathan bakin jini a ciki da wajen Najeriya, musamman idan aka lura da yadda jami’ansa suka rika karyata lamarin a farkon faruwarsa tare da bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na siyasa don bata wa gwamnatinsa suna. Shi kansa Shugaban kasa Jonathan ya yi gum da bakinsa har tsawon kwana 18 da sace ’yan matan kafin ya furta komai, wannan batu da kuma gazawar gwamnatinsa na dakile hare-haren Boko Haram da tashin bama-bamai da sauran matsalolin tsaro da mugun cin hanci da rashawa da ake zargin mukarraban gwamnatinsa da yi, sun taimaka wajen kayar da shi a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris.
kungiyar Amnesty International ta ce akalla mata dubu biyu ne kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya a bara kawai.
kungiyar ta ce mayakan Boko Haram suna garkuwa ne da ’yan matan a dajin Sambisa, wasu kuma ana garkuwa da su ne a tsaunin Gorsi da ke gabar ruwan Tafkin Chadi a cikin Kamaru.
Rahoton na kungiyar Amnesty ya ce kusan mutum 200 da suka hada da mata da ’yan mata 28, da suka tsere daga hannun mayakan, sun bayar da bahasi, inda suka ce su aikinsu shi ne su yi harbi su yanka mutane ko su kashe su.
kungiyar ta kuma bayyana yadda ake shigar da maza da kananan yara cikin kungiyar da karfin tsiya ko a kashe su, yayin da ake kame mata a yi musu fyade ko auren dole.
Kame ’yan matan Chibok su 280, da aka yi ya ja hankulan al’ummar duniya, tare da tallafin kungiyar nan ta #BringBackOurGirls da ta rika jagorantar zanga-zangar neman a sako ’yan matan a Abuja da wani lokacin kuma a Legas.
A cikin wani rahoto da Amnesty ta fitar, wata yarinya da ta tsere daga hannun mayakan Boko Hara, kuma aka zanta da ita, ta ce mayakan sun yi mata fyade sau da dama, wani lokaci ma taron dangi suke yi mata.
Amnesty ta ce tana son a kaddamar da binciken kan aikata laiffufukan yaki da mayakan Boko Haram suka yi, yayin da rahoton kungiyar ya kiyasta cewa sama da mutum 4000 suka mutu sanadin ayyukan Boko Haram kawai a bara.
Yarinyar nan mai gwagwarmayar samar da ilimi ga yara mata a duniya, mai suna Malala Yousafzai ta soki yadda hukumomin Najeriya da shugabannin duniya ke jan kafa wajen ceto ’yan matan na Chibok daga hannun mayakan kugiyar Boko Haram, wadanda suka yi awon gaba da su a bara.
Sukan na Malala ya zo ne ranar Litinin kwana daya kafin cika shekara daya da sace daliban mata da yawansu ya zarce 200.
A wata wasika da ta aika wa hukumomin, Malala ta ce, a ganinta Najeriya da shugabannin duniya ba su yi cikakken kokarin ceto ’yan matan ba daga hannun kungiyar Boko Haram ba.
A wasikar, Malala ta ambaci ’yan matan da sunan ’yan uwanta jarumai, inda kuma ta nanata cewa tana cikin dimbin jama’ar da ke gwagwarmayar ceto su.
A dayan bangaren kuma, Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa, kimanin kananan yara dubu 800 ne aka raba su da gidajensu a Najeriya sakamakon ta’addancin kungiyar Boko Haram.
…Gwamnati ba ta yi watsi da ’yan matan Chibok ba – Omeri
Ko’odinetan Cibiyar Bayara da Bayanai ta kasa (NIC) kuma Daraktan Hukumar Fadakarwa Mista Mike Omeri ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta yi watsi da ’yan matan Chibok fiye da 200 da aka sace a Jihar Borno shekara guda da ta gabata ba.
Ya ce, har yanzu ana ci gaba da aikin gano ’yan matan, kuma an mayar da hankali wajen zakulo ’yan matan a wuraren da ake zaton ana rike da ’yan matan.
Omeri wanda ya nuna damuwa kan sace ’yan matan ya ce, gwamnati ta bullo da dimbin dabaru da kuma sadaukar da dimbin albarkatu tare da nemo tallafi daga kasashen duniya musamman makwabtan kasar nan da kungiyoyin kasashen duniya domin tabbatar da an kubutar da ’yan matan tare da mayar da su ga iyalansu lafiya.
“Abin bakin ciki ne sace ’yan matan, kuma babban abin bakin ciki shi ne yadda muka kasa ceto ’yan matan – ko wadanda suka sace su suka gaza mayar da su wurin iyayensu, sai dai abin da yake fili kuma yake da tabbaci gwamnati ba ta yi watsi da binciko inda ’yan matan suke ba, maimakon haka gwamnati tana zuba dukiya da albarkatu fiye da yadda ake zato a kan lamarin,” inji Omeri.
Ya kara da cewa, “Ba ta yi watsi da binciken ba, ba ma kawai ta kwato yankuna ba, tana son ta ceto mutanen da aka sace, wanda ake samun nasara a cikin mako shida ko fiye.”
Game da da’awar da sojoji suka yi cewa sun san inda ’yan matan suke, Omeri ya ce: “Ba zan yi magana a madadin sojoji ba kan batun sanin inda ’yan matan suke ba, amma na san sojoji kamar sauran ’yan Najeriya da sauran jama’a sun san suna wani yanki ne kamar yadda ko su ’yan ta’addan suka yi da’awa – wato dajin Sambisa, wanda kowa ya san nan ne wurin kuma wannan ne ya sa a yau aka mayar da hankali kan dajin Sambisa. An mayar da hankali kan wannan yanki har zuwa duwatsun Kamaru. Don haka ina jin an mayar da hankali sosai a wannan yanki da ake zargin nan ne ’yan matan suke.”
Game da rahoton da Majalisar dinkin Duniya ta fitar cewa mai yiwuwa mayakan kungiyar sun kashe ’yan matan a garin Gwoza, Omeri ya ce, ba za a san yawan mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe ba, har sai an gama kwato garuruwan da suke hannun Boko Haram inda ’yan matan suke. Kuma ya ce babu wata shaida da ke nuna an kashe ’yan matan, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an gano ’yan matan.
“Babu wanda zai fidda rai, saboda ’yan matan nan ’yan Najeriya ne. Ba kasa ce marar kan gado ba; mu mutane ne da suke son makwabtanmu, mutanen da suke da dabi’u masu kyau, don haka ana ci gaba da bincike har sai an gano ’yan kasarmu, don haka babu wanda zai fidda rai,” inji Omeri.
…Za mu ceto ’yan matan Chibok idan suna raye sai dai … –Buhari
Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya ce za su yi bakin kokarinsu don ceto ’yan matan Chibok fiye da 200 da mayakan Boko Haram suka sace idan suna raye sai da ya ce ba zai yi alkawarin yaushe zai kubutar da su ba, saboda har yanzu ba a san inda ake garkuwa da su ba.
Janar Buhari ya fadi haka ne a ranar Talata ranar da aka yi juyayin cika shekara daya da sace ’yan matan.
A cikin sanarwar da ya fitar, Janar Buhari ya ce amma gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta domin ganowa da mika ’yan matan ga iyayensu.
Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya sha daukar alkawarin kubutar da ’yan matan ba tare da samun nasara ba.
Amma Janar Buhari wanda ya kayar da Jonathan a zaben Shugaban kasa ya ce akwai bukatar fadin gaskiya a kan makomar ’yan matan da kuma yaki da Boko Haram.
Janar Buhari ya ce a ranar Talatar cewa “Yau rana ce ta bakin ciki da jimami a kan halin da ’yan matan da iyayensu ke ciki.”
Fiye da 50 daga cikin ’yan matan da mayakan Boko Haram din suka sace a bara, an samu bayanin ganinsu da rai kimanin mako uku da suka gabata, kamar yadda wata mace ta shaida wa gidan rediyon BBC.
Matar wadda ba ta so a ambaci sonata ba saboda tsaron rayuwarta ta shaida wa BBC cewa ta ga ’yan matan a Gwoza kafin sojojin gwamnati su fatattakin mayakan Boko Haram daga garin. Ta ce, ta zauna a garin ne lokacin da yake karkashin ikon Boko Haram, kuma ta rika ganin ’yan matan da suturu na Musulunci bisa rakiyar mayakan.
“An ce ’yan matan Chibok ne da aka tsare a wani babban gida. Kuma muna kusa da gidan da ke tsallake hanya,” inji ta.
Wata matar ta shaida wa BBC cewa ta ga wasu daga cikin ’yan matan wadanda shekarunsu suka kama daga 16 zuwa 18 a karo na karshe a watan Nuwamban bara a wani sansanin ’yan Boko Haram da ke kauyen Bita da ke Arewa maso Gabas din.
“Kimanin mako daya bayan an kawo su sansanin, daya daga cikinmu ta leka ta wani taga, ta ce: “Da gaske ku ’yan matan Chibok ne?” su kuma suka ce “Eh.” Mun gaskata su kuma ba mu sake tambayarsu ba,” inji matar.
Wasu mata uku ma sun shaida wa BBC cewa sun ga ’yan matan a garin Gwoza, garin da ake da yakinin Boko Haram sun mayar da shi hedkwatar daular da suka yi ikirarin kafawa bayan sun kwace shi a watan Agustan bara.
Sojojin Najeriya da ke samu tallafa daga sojojin Kamaru da Chadi da Nijar sun kwato garin a watan Maris din da ya gabata. Kuma an ce mayakan Boko Haram da dama sun gudu zuwa dutsen Mandara da ke iyaka da kasar Kamaru, to amma babu tabbacin sun tafi da ’yan matan ko a’a.
…’Yan matan Chibok suna nan a raye – Salkida
Wani dan jarida – da aka san yana da dangantaka ta kut-da-kut da shugabannin Boko Haram – ya ce ’yan matan Chibok fiye da 200 da kungiyar ta sace suna nan a raye, kuma cikin koshin lafiya.
A wata hira ta musamman da Ahmad Salkida ya yi da BBC, ya ce ’yan matan na da matukar muhimmanci a wurin kungiyar ta Boko Haram saboda, a cewarsa, sun amince da akidojinta.
Ahmed Salkida ne dan jarida daya kacal da ya ziyarci dajin da ’yan Boko Haram suke tsare da ’yan matan bayan an sace su, lokacin da ya yi yunkurin shiga tsakanin ’yan Boko Haram da gwamnati domin ganin an kubutar da su.
Ya yi ikirarin cewa an yi watsi da batun shiga tsakanin da ya so ya yi bisa umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na dakatar da hakan.
Sai dai gwamnatin ta sha cewa a shirye take ta bi duk wata sahihiyar hanya ta sulhuntawa da kungyar ta Boko Haram.