’Yan matan Chibok bayan ziyarar Malala…

“Shugaban kasa ya sake jaddada takaicinsa akan halin da `yan matan Chibok suke ciki, da kuma goyon bayansa na ganin lallai an ceto `yan matan, sun dawo gidajensu cikin koshin lafiya. Yana da zabi da yawa, amma babban zabinsa shi ne irin yadda za a kubutar da su lami lafiya, su kuma dawo wajen iyayensu […]

’Yan matan Chibok bayan ziyarar Malala…
’Yan matan Chibok bayan ziyarar Malala…

“Shugaban kasa ya sake jaddada takaicinsa akan halin da `yan matan Chibok suke ciki, da kuma goyon bayansa na ganin lallai an ceto `yan matan, sun dawo gidajensu cikin koshin lafiya. Yana da zabi da yawa, amma babban zabinsa shi ne irin yadda za a kubutar da su lami lafiya, su kuma dawo wajen iyayensu lafiiiya kalau.” Wadannan kalamai na daga cikin kalaman da `yar kasar Paakistan din nan mai rajin kare hakkin ilmin mata, Malala Yousatzai,`yar shekaru 17 da haihuwa, ta gabatar a Abuja a cikin ziyarar kwanaki biyu da ta kawo kasar nan a wancan makon, a cikin gwagwarmayar da ake yi wajen ganin an ceto sauran `yan matan Chibok 219, da `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid da`awati Wal jihad da ake kira Boko Haram suka sace a Sakandaren `yan mata ta Chibok, a jihar Barno yau kwanaki 102.
A yayin ziyarar Malala din, wadda ta shigo Abuja a cikin jagorancin mahaifinta, bisa ga amsa gayyatar shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, masu kula da al`amurran da ka je su komo, sun  fassara makasudin ziyarar a zaman kamfen da neman daga matsayin gwamnatin tarayya a idanun `yan kasa da na waje akan kokarin da take yi wajen ganin ta ceto `yan matan da aka sace tun ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata.
Ita dai wannan budurwa Malala sunanta ya bayyana a duniya, yau sama da shekaru biyu, tun bayan da `yan kungiyar Taliban a kasar Pakistan, kungiyar da ita ma take gwagwarmaya akan hana `ya`ya mata karatun boko  a kasar, suka fahimci gwagwarmayarta, suka kuma bita har cikin mota suka harbe a ka, da aniyar su kasheta, amma Allah Ya sa tana da sauran shan ruwa, bayan jiyyar da ta sha a cikin kasar ta ta Pakistan da kuma wani shararren assibiti na kasar Birtaniya, ta samu lafiya. Tun daga wancan lokaci kasashen Amurka da na Turai da sauran kungiyoyin duniya masu rajin kare ilmi `ya`ya mata da hakkin bil Adama da kafofin yada labaran kasashen waje, suka mayar da hankali akanta, har take kokarin ta zama babbar mai rajin kare hakkokin ilmin mata da sauran hakkokin kananan yara. Kai karewa ma da karau, har Majalisar dinkin duniya ta je ta kuma hau mumbarin da shugabannin kasashen duniya suke jawabi, ta kuma yi  jawabi, akan rajin kare ilmin `ya`ya mata da sauran hakkokin kananan yara, musamman akan ilmi.
A lokacin ziyarar Malala ta kwana biyu a kasar nan, ta samu ganawa da shugaban kasa da wasu `yan matan Chibok 5, daga cikin wadanda suka samu kubutowa daga hannun `yan Boko Haram da iyayensu 11, da kuma `yan kungiyar #BringbackOurGirls, wacce ta ke fafutikar matsa wa gwamnati lamba don ganin ta kubutar da sauran `yan matan. Kamar yadda Malala ta shaida wa wani taron manema labarai, a saduwarta da shugaba Jonathan ta fadi cewa shugaban kasar ya yi mata alkawarin zai bayar da guraben karo ilmi har ya zuwa jami`a a cikin kasar nan ga dukkan `yan matan na Chibok da aka sace. Sannan kuma ya sha alwashin zai gana da iyayen `yan matan da aka sace (ganawar da idan kome ya tafi yadda aka tsara to, an riga an yi ta tun ranar Talatar da ta gabata a Abuja). Duk kuwa da irin yadda iyayen yaran suka fi son cewa shugaba Jonathan ya taras da su ne a garin na Chibok, inda zai yi musu jaje, sannan kuma ya fayyace masu dalla-dalla irin kokarin da jami`an tsaron gwamantinsa da sauran kasashen duniya suke yi wajen ganin sun kubuto da `ya`yansu.
Ga wasu `yan kasa suna ganin waccan ganawa ta zo a makare idan aka yi la`akari da irin dogon lokacin da aka dauka yau sama da watanni uku ba a yi ta ba, yanzu din ma masu irin wancan ra`ayi na ganin albarkacin ziyarar Malala din aka yi ta. Dangane da kome shugaban kasa zai fadawa iyayen `yan matan, da bai taba fada ba tunda aka sace su? Masu irin wannan ra`ayi na ganin kome zai fadawa iyayen `yan matan ba shi da wani muhimmanci ga iyayen da gwamnatin Jihar Barno da ma `yan kasa, musamman `yan kungiyar #BringOurgirlsBack, da ya wuce takamaiman shirin da jami`an tsaron gwamantinsa da na kasashen waje irin su Amurka da Birtaniya da Isra`ila da sauransu suke yi wajen ganin an kubuto sauran `ya`yansu, cikin koshin lafiya, dukkan bayanan da suka saba haka, to, ba za su zama masu karbuwa da gamsarwa ba ga mutanen Chibok din da sauran `yan kasa.
Kazalika, bayan samun wancan tabbaci wanda zai saba wa wadanda ya yi ta yi a baya, akwai kuma bukatar a ce ya nemi afuwarsu, bisa ga irin tun farko shakkun da ya samu na cewa ba a ma sace `yan matan ba, da kuma bisa ga kin zuwa Chibok don jaje, bare kuma ya ga irin yadda garin yake kokarin ya zama kufai, a dalilin rikicin na `yan kungiyar ta Boko Haram da alkawarin tallafin da gwamnatinsa za ta yi musu wajen sake tsugunnar da su da ma sauran garuruwa da kauyukan da ke shiyyar Arewa maso Gabas da annobar ta Boko Haram ta dai-daita.
Ya yin da wasu suke da ra`ayin ziyarar ta Malala ba ta da wani amfani. Ni a ra`ayi na tana da matukar amfani da tasiri, ba don komeai ba, amincewar da shugaba Jonathan ya yi bayan watanni uku da sace `yan mata na cewa zai ma yarda ya gana da iyayen `yan matan da alkawarin ba su guraben karo ilmi har jami`a, su kansu wasu abubuwa ne da Malala ba ta zo ba, ba zai yi alkawarinsu ba.
A gefe daya kuma ziyarar ta kara bayyana irin raunin shugabancin da aka dade ana zargin gwamnatin shugaba Jonathan take da shi, bisa ga irin yadda ya sa aka kashe makudan kudin kasar nan don gayyato Malala ’yar shekaru 17, a duniya, don kawai ta zo ta sadu da `yan matan Chibok da iyayensu, ta kuma furta albarkacin bakinta akan rashin dacewar tashe-tashen hankula da kashe-kashe da `yan kungiyoyi irin na Taliban da Boko Haram suke haddasawa a cikin kasashen duniya. Kamar dai yadda shugabannin al`umma da na siyasa a kasar nan suka dade suna yi.
Malala dai ta zo ta gani ta koma ta kuma barmu da matsalolinmu. Babban aiki ya rage garemu don ba wanda zai mana maganinsu, sai mu da taimakon Allah. Shugabanni da dukkan `yan kasa ya kamata kowa ya tashi tsaye ya kamanta gaskiya da adalci, amma in haka za mu zauna sai an kawo Malala dubu suna zuwa suna tafiya suna barin mu da matsalolinmu.