’Yan matan Chibok: Ina aka kwana bayan shekara 7?
Shekara 7 bayan sace ‘yan matan Chibok, masu fafutuka sun ce sun yi wasu nasarori
Kusan shekara bakwai ke nan cur tun bayan da wasu mata suka taru a dandalin Eagle Square da ke Abuja, don kira ga gwamnati ta yi wani abu game da ’ya’yansu da aka sace.
Wadannan mata mambobi ne a reshen Abuja na Kungiyar Raya Yankin Chibok (KADA) kuma sun taru ne don yin zanga-zangar lumana bayan sace ’yan mata 230 daga wata makaranta a garin Chibok na Jihar Borno.
’Yan sanda dai sun tarwatsa matan, amma kwanaki kadan bayan haka aka gudanar da wani gangami da aka yi wa taken “Macin Mata Miliyan Daya”, wanda ya haifar da kungiyar #BringBackOurGirls.
- Abin da ya sa nake sana’ar tukin Keke Napep —Amina “Sai Mama”
- Yadda na sauya akalar marigayi Ibro –Falalau Dorayi
A wadannan shekaru, ’ya’yan kungiyar KADA mata da maza sun bi tafiyar #BringBackOurGirls an ci gaba da gwagwarmaya da su.
A wannan bidiyon, jami’in yada labarai na kungiyar ta KADA ya bayyana nasarorin da yake ganin gwagwarmayar ta haifar da kuma takaicinsu game da wannan lamari.
Za kuma ku iya kallon bidiyon a shafinmu na YouTube.