’Yan matan Chibok: Katobarar matar Shugaban kasa ta tada kura
Uwargidan Shugaban kasa, Misis Patience Jonathan ta fusata ’yan Najeriya bayan da ta nuna shakku kan kame ’yan mata ’yan makaranta 276 a wata sakandaren Chibok da ke Jihar Borno da kuma yadda ta ba da umarnin a kama biyu daga cikin matan da ke jagorantar zanga-zangar neman a sako ’yan matan tare da yi […]

Uwargidan Shugaban kasa, Misis Patience Jonathan ta fusata ’yan Najeriya bayan da ta nuna shakku kan kame ’yan mata ’yan makaranta 276 a wata sakandaren Chibok da ke Jihar Borno da kuma yadda ta ba da umarnin a kama biyu daga cikin matan da ke jagorantar zanga-zangar neman a sako ’yan matan tare da yi musu kazafin kasancewa ’yan Boko Haram.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Uwargidan Shugaban kasar ta fara wannan katobara, inda ta kalubalanci Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya fito da ’yan matan da aka sace daga makarantar, inda ta ce idan zuwa Lahadi ba a gano su ba, za ta jagoranci zanga-zanga zuwa Maiduguri domin neman bayani kan inda suke daga Gwamnan.
Misis Patience Jonathan, wadda ta bayyana haka bayan ganawa da matan gwamnoni da ’yan majalisar tarayya mata da na jihohi da wasu shugabannin kungiyoyin mata a daidai lokacin da mijinta Shugaba Jonathan ke ganawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar Shugaban kasa, wadda ta dage taron zuwa karfe 4:00 na yammacin Lahadi ta ce a matsayin gwamnoni na manya jami’an tsaro na jihohinsu, wajibi ne su dauki alhakin tsaron jihohin nasu.
“Kuma zuwa Lahadi, muna son ganin ’ya’yanmu. Idan ba mu samu ba, za mu yi tattaki zuwa Borno, mu tuhumi Gwamnan ya ba mu ’ya’yanmu. Za mu yi jerin gwano zuwa majalisar dokoki don ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa, kuma za mu yi jerin gwano don ganin Shugaban kasa”, inji ta.
Kalaman na Misis Jonathan ba su yi wa dattawan Jihar Borno dadi ba, inda suka mayar da martani cewa ta kama mijinta Shugaba Jonathan kan laifin sace daliban, domin shi ne babban jami’in tsaron Jihar Borno.
Kakakin dattawan, Bulama Mala Gubio ya ce matar Shugaban kasar ta yi magana ne cikin jahilci, saboda Jihar Borno tana karkashin dokar ta-baci, kuma hakan ya sa an kwace iko da jami’an tsaro daga hannun Gwamnan, an mika wa Shugaban kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yake amfani da wannan iko ta hannun Babban Hafsan Tsaro ko Hafsan Hafsoshin Sojan kasa.
Sai dai kuma a maimakon matar Shugaban kasar ta jagoranci zanga-zangar da ta yi barazana, sai ga shi a ranar Litinin ta buge da nuna shakku kan sace daliban, tare da bayar da umarnin kama jagororin matan da ke zanga-zangar neman a sako ’yan matan. Sai dai Kakakinta Ayo Adewuyi ya ce ba ya da masaniya kan wannan umarni, inda ya ce, “Uwargidan Shugaban kasa ba ta bayar da umarnin tsare kowa ba, kuma ina da tabbacin haka,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP.
Sai dai a cewar daya daga cikin shugabannin zanga-zangar, Misis Saratu Angus Ndirpaya, wadda ta fito daga garin Chibok, ta ce jami’an tsaro na SSS sun kama ta ita da jagorarsu, Misis Naomi Mutah Nyadar, inda suka kai su wani ofishin ’yan sanda a ranar Litinin bayan sun kwana suna ganawa a fadar Shugaban kasa. Ta ce ’yan sandan sun hanzarta sakin ta, amma suka ci gaba da tsare Naomi Nyadar.
Misis Ndirpaya ta ce Misis Jonathan ta zarge su da kirkirar karya kan kame daliban. “Ta fadi karairayi da dama, cewa muna son bata sunan gwamnatin Najeriya ne, kuma ba mu son goya baya ga mulkin mijinta,” kamar yadda ta shaida a AP ta tarho.
Ta ce sauran matan da ke wurin taron sun goya wa matar Shugaban kasar baya, ciki har da jami’an gwamnati da na Jam’iyyar PDP, wadanda suka rika cewa: “Haka ne, haka ne!” a duk lokacin da Misis Jonathan ta zarge su da kasancewa ’yan Boko Haram. “Sun ce mu ’yan Boko Haram ne, kuma Misis Nyadar ’yar Boko Haram ce.” Ta ce ita da Nyadar ba su da ’ya’ya a cikin wadanda aka sace, amma suna goyon bayan iyayen ’yan matan da aka sace ne.
Wata katobarar da matar Shugaban kasar ta yi ita ce ta cewa matan “ba su da ’yancin yin zanga-zangar,” musamman Nyadar, wadda ta gano Mataimakiyar Daraktar Hukumar Samar da Aiki (NDE) ce, inda Misis Jonathan din ta ce ta ajiye aikin gwamnati, kamar yadda Ndirpaya ta ce.
Sai kuma umarnin da ta bayar cewa dukkan matan Najeriya su daina zanga-zanga, inda ta yi barazanar cewa, “Duk abin da ya same su, a lokacin zanga-zanga, kada su yi kuka da kowa sai kansu,” kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A nata martanin, babbar jam’iyyar adawa APC ta nuna kaduwa kan yadda Uwargidan Shugaban kasar take yin wannan katobara, inda ta ce ya kamata ta fahimci cewa mijinta ne babban jami’in tsaron kasa, kuma ta fahimci cewa Jihar Borno inda aka sace ’yan matan na karkashin dokar ta-baci, mijinta ya zama babban jami’in tsaron jihar, don haka kuskure ne ta yi barzanar zanga-zangar zuwa Borno don neman Gwamnan ya fito da yaran. “Kamata ya yi ta yi zanga-zanga zuwa Fadar Shugaban kasa a maimakon haka,” inji APC.
Jam’iyyar APC ta nuna mamakinta kan a ina matar Shugaban kasar ta samu karfin ikon gayyatar zababbun shugabanni da nadaddu zuwa Fadar Shugaban kasa, domin tuhumarsu kan bacewar ’yan matan. Ta ce ta hanyar haka ta kwace aikin da tsarin mulki ya ba Shugaban kasa, tare da mayar da shi marar katabus wajen iya gudanar da harkokin kasar nan, lamarin da ya sa Najeriya ta zama abar dariya a idon kasashen duniya.
“Matar Shugaban kasa ta yi sammacin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno da DPO din Chibok da Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno da Shugaban karamar Hukuma da shugabar makarantar da lamarin ya faru da mai gadin makarantar. A ina ta samu ikon yin wannan sammaci? Shin ta san illar sanya jami’an tsaro su rika bayani ga jama’a ta talabijin, muhimman bayanan da za su iya kawo cikas ga yunkurin gano ’yan matan? Yaya Kwamishinan ’Yan sanda, wanda ke samun umarni daga Gwamnan Jiha, zai koma karkashin Uwargidan Shugaban kasa? A ina ne a tsarin mulki ko a cikin wata doka Uwargidan Shugaban kasar ta samo irin wannan iko?” APC ta tambaya.
kungiyoyi na ci gaba da nuna bacin rai kan yadda Uwargidan Shugaban kasar take wannan katobara, musamman barazanar da ta yi ga mata masu zanga-zangar neman a sako ’yan matan da aka sace.
Wannan kura tana tashi ne a daidai lokacin da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi barazanar zai sayar da ’yan matan tare da ci gaba da kai hari ga makarantu don ci gaba da kame dalibai mata.
Shekau, wanda ya fitar da faifan bidiyo yana ikirarin sace ’yan matan, ya bayyana ’yan matan da suka sace da cewa bayi ne, kuma zai sayar da su a kasuwa.
An rika bayar da rahotannin cewa ana daura wa ’yan matan aure kan sadakin Naira dubu biyu, inda ake zargin an tsallaka da wasu zuwa kasashen Kamaru da Chadi. Kuma wani mai shiga tsakani kuma malamin addinin Musulunci da ya nemi a boye sunansa ya ce, ’yan Boko Haram din a shirye suke a biya su fansa kan ’yan matan, kuma ya ce biyu daga cikin ’yan matan sun mutu sakamakon sarin maciji, yayin da 20 suke fama da jinya, kamar yadda kafar labarai ta Premium Times ta ruwaito.
A ranar Talata, ’ya’yan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari a garin Gambouru inda suka halaka mutum 200, ciki har da ’yan sanda 16, yayin da suka sake sace ’yan mata 11 a kauyen Wala da ke karamar Hukumar Gwoza.
Kame dimbin ’yan matan da gazawar sojojin Najeriya su kwato su, ta haifar da bacin rai da korafe-korafe da suka jawo zanga-zanga a fadin kasar nan. Masu zanga-zangar suna zargin Shugaba Jonathan da nuna halin ko-in-kula da halin da ’yan matan ke ciki.
Tuni zanga-zangar ta fara yaduwa a wasu kasashen duniya, yayin da wasu fitattun mutane, ciki har da Uwargidan Shugaban Amurka, suka rika sanya rigunan da suke dauke da taken: “A dawo mana da ’yan matanmu.”