’Yan matan Chibok na garin Gwoza – Wadda ta kubuta
Wata mace mai shekara 56 mai suna Mbutu Papka, da mayakan Boko Haram suka sace a watan Yulin bara kuma suka tsareb a sansanoni biyu na tsawon wata takwas ta ce tabbas ’yan matan Chibok suna nan cikin tsaro a wani gida a garin Gwoza da ke Jihar Borno. Matar ta samu kanta daga hannun […]
Wata mace mai shekara 56 mai suna Mbutu Papka, da mayakan Boko Haram suka sace a watan Yulin bara kuma suka tsareb a sansanoni biyu na tsawon wata takwas ta ce tabbas ’yan matan Chibok suna nan cikin tsaro a wani gida a garin Gwoza da ke Jihar Borno.
Matar ta samu kanta daga hannun Boko Haram ne a kwanakin baya, inda ta bayyana wa wata kafar labarai mai bin diddigi (International Centre for Inbestigatibe Reporting – icirnigeria.org) cewa an tsare ta a wuri guda da ’yan matan Chibok din.
Papka ta ce ba a barin kowa ya je kusa da katangar gidan da ake tsare da ’yan matan wadanda ake gadinsu dare da rana. Ta ce hatta masu tsaron ’yan matan da ke dauke da miyagun makamai ana kyale su ne kawai su shiga gidan don kai musu abinci.
Matar wacce aka kame tare da wasu lokacin da Boko Haram suka kai hari Gwoza ranar 4 ga Yulin bara an kai su kauyen Mdita, da ke kusa da dajin Sambisa da ke iyakar Askira Uba da Damboa da kuma Gwoza.
Wadanda aka sacen sun hada da yara da dama kamarb yadda Papka ta ce, kuma an ajiye su a kauyen Mdita na tsawon wata biyar kafin a mayar da su Gwoza inda aka tsare su na wata uku kafin a karshe a sake su ranar 15 ga Maris din nan.
Ta ce, lokacin da take Gwoza ne ta samu bayanin cewa ’yan matan Chibok da sace su ya jawo hankalin kasashen duniya suna tsare a wani gida da ke kusa da inda ita ma aka tsare su.
Da aka tambaye ta yaya aka yi ta san ’yan matan suna can, sai Papka ta ce ba ta ga ’yan matan Chibok ba, amma ta ce mutanen da ke yankin sun nuna mata cewa wancan gida da ake matukar kula da tsaronsa a cikin ’yan matan suke. Kuma ta ce saboda takaita shiga gidan ya sa ’yan matan ne suke girki da kansu da sauran ayyukan da suka shafe su.
A ranar 15 ga Maris bayan wata uku a Gwoza ne, Papka da wasu tsofaffin mata 10 aka raba su da sansani, inda aka sanya su a wata mota aka kai su kauyen Izge inda daga nan aka kai ta kauyenta a kan babur saboda rashin kyan hanya. Sai dai ta ce ba a kyauta aka kai ta a babur din ba, “An bukaci in biya Naira dubu takwas kudin kai ni a babur, inda na karba daga dangina,” inji ta.