’Yan matan Chibok: Shekara guda ba amo, ba labari
A ranar Talatar da ta gabata ne ’yan matan garin Chibok su fiye da 200 suka cika shekara guda bayan ’yan Boko Haram sun sace su a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok na Jihar Barno. ‘Yan matan sun je makarantar ne saboda jarrabawar kammala sakandare da za su rubuta, inda daga ranar ne […]
A ranar Talatar da ta gabata ne ’yan matan garin Chibok su fiye da 200 suka cika shekara guda bayan ’yan Boko Haram sun sace su a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok na Jihar Barno. ‘Yan matan sun je makarantar ne saboda jarrabawar kammala sakandare da za su rubuta, inda daga ranar ne aka tilasta masu tafiyar da ba a kara jin duriyarsu ba har yanzu. Akwai batun da ke cewa an aurar da su a matsayin bayi. Wannan batun ya jawo alhini daga ciki da wajen kasar nan.
Babbar tambayar ita ce ina ’yan matan suke? Dubban mutane sun mutu sakamkon rikicin Boko Haram. Shin ko ’yan matan suna cikin wadanda suka rasa rayukansu? Ko kuwa suna wani wuri ne a boye da ransu, amma ba tare da an san halin da suke ciki ba?
Tun bayan da aka sace su akwai karuwar fargabar halin da suke ciki. Halin ko ina kular da gwamnati ta nuna da kuma ci gaba da yunkurin ceto su ya kara jefa alhini a zukatan ’yan Najeriya musamman ma dangin ’yan matan. Wasu daga cikinsu sun shiga cikin mawuyacin sakamakon tashin hankalin da ke tattare da rashin samun masaniyar wurin da ’ya’yansu suke da kuma rashin masaniya kan halin da suke ciki.
Har ila yau, halin ko ina kular da Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna kan tabarbarewar tsaro, inda a makon da aka sace ’yan matan aka kai hari a tashar motar Nyanya da ke Abuja, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar dimbin rayuka. Hakan ya sanya shugabanni da fitattun mutane a duniya suka fara nuna goyon bayansu ga maudu’in da ke kira da a ceto ’yan matan wato #BringBackOurGirls, taken da ya karade ko ina duniya. Lamarin ya nuna yadda gwamnati da manyan jami’anta da na jam’iyya mai mulki ba su da damu ba kuma ba sa aikin da aka dora masu na kare kasar nan da kuma rayuwar jama’ar da ke cikinta.
Da farko gwamnatin ba ta yarda cewa an sace ’yan matan ba, kuma daga nan ne wasu suka fara yada zargin cewa an sace su ne domin a nuna gazawar gwamnatin Shugaba Jonathan.
Jama’a sun bayyana damuwa sosai lokacin da aka samu labarin cewa kwana biyu kafin faruwar al’amarin an samu bayanan sirri da ke bayyana hakan, amma sai gwamnati ta yi biris. Har ila yau, saboda yadda wasu jami’an gwamnati suke goyo bayan gwamnati da kuma adawa karara da masu fatan an ceto ’yan matan daga masu garkuwa da su. An kirkiri wata kungiya da zama kishiya ga ta masu fafutukar ganin an ceto ’yan matan saboda a kashe karsashin kungiyar ta ainihi a idanun jama’a.
Duk domin haddasa rudani, rudunar soji kasar nan da ke yaki da ’yan Boko Haram ta dinga bayyana bayanai masu cin karo da juna dangane da wurin da ’yan matan suke boye da halin da suke ciki, inda a wani karo ta bayyana kubutar da galibinsu.
Kodayake, rundunar sojin ta kai farmaki sansanoni da mabuyar ’yan gwagwarmayar, amma ba tare da samun masaniyar kan halin da ’yan matan suke ciki ba. Al’amarin bacewar ’yan matan abu ne da zai dade bai bace ba a zukatan ’yan Najeriya da kuma sauran jama’a a fadin duniya musamman saboda wannan wata gazawa ce daga bangaren wannan gwamnatin ko da ko ’yan matan sun samu kubuta daga hannun masu garkuwa da su a yau, ko a nan gaba. Har ila yau, bacewar ’yan matan shi ne ya ankarar duniya ayyukan ta’asar da kungiyar Boko Haram take aikatawa.
Zababben Shugaba Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwmnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen samar da tsaro ciki har da magance rikicin Boko Haram. Da a ce Shugaba Jonathan ya dora daga inda marigayi Umaru Musa ’Yar’Adua ya tsaya, wato aiki tukuru wajen yakar ayyukan ta’addanci da wannan bai ma taso ba. Amma bai yi hakan ba, wannan ya sa ake ci gaba da tambayar, ina ’yan matan Chibok? Tambaya ce kuma da har yau ake bukatar amsarta.