’Yan matan Chibok sun cika kwana 200 a hannun ’yan Boko Haram
A yau Juma’a ne ’yan matan makarantar Sakandaren Chibok da ’yan Boko Haram suka sace suke cika kwana 200 a hannunsu. A ranar 14 ga watan Afrilun da ya wuce ne ’yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da ’yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok da ke Jihar Barno, kodayake akwai rahotannin da […]
A yau Juma’a ne ’yan matan makarantar Sakandaren Chibok da ’yan Boko Haram suka sace suke cika kwana 200 a hannunsu.
A ranar 14 ga watan Afrilun da ya wuce ne ’yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da ’yan mata 276 a makarantar Sakandaren Chibok da ke Jihar Barno, kodayake akwai rahotannin da suka ce 50 daga ciki sun kubuta.
Tun lokacin dai ba a yi wani gagarumin kokari na ganin an kubutar da sauran ba. Sai dai zarge-zarge da alkawuran ceto su da ba a kai ga cika su ba. Kazalika, lokacin da kasar Amurka da Birtaniya suka shigo kasar nan domin taimakawa a fafutukan ganin an ceto su, an samu kwarin gwiwa sosai, sai dai har yanzu shigowar tasu ba ta haifar da da mai ido ba.
A bangare guda iyalan ’yan matan na ci gaba da kasancewa cikin tsananin damuwa, inda hakan ya yi sanadin mutuwar iyaye bakwai daga cikinsu. Saura kuma suka fara fitar da rai game da gano ’ya’yan nasu kwana 200 bayan sace su.
Bayan sace ’yan matan ne kuma mayakan kungiyar Boko Haram suka rika kai miyagun hare-hare da suka kwace garuruwa sama da 10 a jihohin Barno da Yobe da Adamawa.
Kwanaki kadan da sace daliban, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fito cikin wani faifan bidiyo tare da wasu daga cikin ’yan matan, yana cewa matan sun zamo bayinsu, kuma ba za a sako su ba sai “gwamnati ta sako ’yan uwansu da suke daure a gidajen yarin kasar nan,” inji shi.
Sace ’yan matan ya sa duniya ta yi ca wajen nuna goyon baya ga ’yan matan a karkashin wani kamfe mai suna #BringBackOurGirls da ke kara matsin lamba a kan Gwamnatin Tarayya ta yi wani abu domin kwato su. Kamfen din ya samu goyon baya daga manyan mutane a fadin duniya, ciki har da uwargidan Shugaban Amurka, Michelle Obama.
A watan Yulin da ya wuce ne kuma yarinyar nan ’yar kasar Pakistan, Malala Yousafzai, ta ziyarci kasar nan inda ta gana da Shugaba Goodluck Jonathan kan batun ’yan matan. Kuma bayan ziyarar ce, Shugaban ya gana da iyayen ’yan matan da wasu daga cikin ’yan matan da suka kubuta a karon farko, kamar yadda Malalar ta bukace shi.
To, sai dai kwana 200 da sace su, har yanzu ba wata alama da ke tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gab da ’yantar da su. Wannan ya sa masu zanga-zangar neman ganin an ceto ’yan matan, ke ci gaba da matsa kaimi inda a ranar 15 ga watan nan suka yi yunkurin isa fadar Shugaban kasa don ganawa da Shugaba Jonathan, amma jami’an tsaro suka hana su isa.
Har ila yau, a ranar 17 ga watan nan ne Babban Hafsan Tsaro Iya Cif Marshal Aled Badeh ya ba da sanarwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Boko Haram a lokacin wani taron hadin gwiwa da suka yi da manyan hafsoshin sojin Kamaru, a Abuja. Kuma an bayyana cewa ’yan Boko Haram za su sako ’yan matan cikin kwana uku, amma yau mako biyu ke nan ba amo, ba labari.
Zuwa yanzu ba wanda zai iya sanin takamaiman halin da ’yan matan suke ciki, balle wurin da suke boye. Kuma wasu na zargin an ketara da su zuwa kasashen Kamaru da Chadi. Wasu rahotanni kuma cewa suke galibin ’yan matan an aurar da su ga mayakan kungiyar Boko Haram, inda sauran kuma suka rasu sakamakon rashin lafiyar da suka yi fama da ita. Babu dai wanda zai iya sanin lokacin da za a ceto ’yan matan. A daidai lokacin da dimbin ’yan Najeriya suke ci gaba da bayyana alhininsu ga iyayen wadanda wannan al’amarin ya shafa.