’Yan matan Chibok sun cika wata 6 a hannun ’yan Boko Haram
A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan matan nan na makarantar Sakandaren Chibok da ’yan Boko Haram suka sace suka wata shida a hannunsu. A ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata ne ’yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da ’yan mata sama da 290 a makarantar Sakandaren Chibok da ke […]
A ranar Talatar da ta gabata ce ’yan matan nan na makarantar Sakandaren Chibok da ’yan Boko Haram suka sace suka wata shida a hannunsu.
A ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata ne ’yan kungiyar Boko Haram suka yi awon gaba da ’yan mata sama da 290 a makarantar Sakandaren Chibok da ke cikin jihar Borno.
Lamarin da ya janyo tofin Allah tsine daga fadin duniya.
Bayan sace ’yan matan ne kuma daga baya mayakan kungiyar Boko Haram suka rika kai miyagun hare-hare da suka kwace garuruwa sama da 10 a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.
Kwanaki kadan da sace daliban, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fito cikin wani faifan bidiyo yana fadin cewa matan sun zamo bayinsu, kuma ba za a sako su ba sai idan gwamnati ta sako ’yan uwansu da suke daure a gidajen wakafi.
Wata ’yar shekara 17 daga cikin daliban da ta samu tserewa daga Boko Haram din ita da wasu daliban biyu daga inda aka fara kai su bayan sace su, ta bayyana wa gidan rediyon Muryar Amurka (bOA) yadda aka yi aka sace su, da yadda suka yi ta cire ’yan kwalinsu suna jefarwa a kan hanya da gangan cikin dare, bisa fatar cewa idan sojoji suka ji labarin an sace su, za su zo su kwace su, kuma za su bi sawun ta ganin inda suka jefar da ’yan kwalinsu.
Ta ce, “Mun yi ta cire ’yan kwalinmu muna jefarwa a kan hanya da yake dare ne, domin in soja suka ji labarin an sace mu, za su iya bin sawu su zo su cece mu. Saboda haka muka yi ta jefar da ’yan kwalinmu a kan hanya cikin dare.”
Sace ’yan matan ya sa duniya ta yi ca wajen nuna goyon bayanta ga ’yan mata a karkashin wani kamfe mai suna #BringBackOurGirls da ke kara matsin lamba a kan Gwamnatin Tarayya ta yi wani abu domin kwato su.
Wannan kamfe ya samu goyon baya daga manyan mutane a fadin duniya, cikinsu har da matar Shugaban Amurka, Michelle Obama.
To sai dai wata shida da sace su, har yanzu ba wata alama da ke tabbatar da cewa hukumomin tsaro na gab da ’yantar da ’yan matan.
Wannan ya sa masu zanga-zangar neman ganin a ceto ’yan matan, ke ci gaba da matsa kaimi, inda a ranar Talata suka yi yunkurin mika wa Shugaba Goodluck Jonatahan wasikar bukatar a ceto ’yan matan, amma jami’an tsaro suka hana su isa fadar Shugaban kasar.