’Yan matan Chibok sun yi kukan yunwa
Wani sabon faifan bidiyo ya nuna yadda ’yan matan Chibok da aka sace suke bayani kan halin kuncin da suka shiga a karon farko, inda suke cewa suna cikin wahala kuma ba su samun isasshen abinci.Wani mai shiga tsakanin gwamnati da ’yan Boko Haram a asirce mai suna Dokta Stephen Dabis da ake tsammanin Shugaba […]

Wani sabon faifan bidiyo ya nuna yadda ’yan matan Chibok da aka sace suke bayani kan halin kuncin da suka shiga a karon farko, inda suke cewa suna cikin wahala kuma ba su samun isasshen abinci.
Wani mai shiga tsakanin gwamnati da ’yan Boko Haram a asirce mai suna Dokta Stephen Dabis da ake tsammanin Shugaba Goodluck Jonathan ne ya dauko hayarsa, ya bayyana haka ga jaridar The Mail on Sunday ta kasar Ingila a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewar jaridar, wadda ke fitowa a shafin intanet, Dokta Stephen, wanda limamin Kirista ne da ya taba zama babban limami a cocin Cobentry Cathedral da ke Landan kuma abokin Achbishop na Canterbury, Justin Welby ne, ya yi kwanaki a Najeriya yana aiki cikin sirri kan sako ’yan matan.
Kuma ta kara da cewa Shugaban kasa ne ya nemi ya zo Najeriya, saboda a baya ya jagoranci kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Gwamnatin Tarayya da ’yan ta’addan Neja-Delta a shekarar 2004.
A wani sakon imel da Dabis ya tura wa jaridar ya bayyana cewa ya samu “hanyar tuntubar” kungiyar da take da hannu a sace mutane a yankin Arewa maso Gabas a shekara bakwai da suka gabata. Kuma ya bayyana nasarar da ya samu wajen kulla yarjejeniya da masu garkuwa da mutane a Najeriya kan “dogon lokacin da ya dauka wajen kulla dangantakar amincewa da juna a tsakanin bangarorin biyu.”
Rahoton jaridar ya ce faifan bidiyon, wanda ba a sake shi ga jama’a ba, amma jaridar ta gani, an dauke shi ne a cikin daji bayan wata daya da sace ’yan matan.
Faifan ya nuna ’yan matan da mayakan Boko Haram suka sace a ranar 14 ga Afrilu, “suna magana da kyar kan halin da suke ciki,” inji rahoton.
Sai dai Aminiya ba ta ga faifan bidiyon ba, don haka ba yadda za ta iya tabbatar da gaskiyar lamarin.
A cewar jaridar Mail on Sunday, a cikin bidiyon ’yan mata takwas da suke sanye da kayan makarantarsu mai launin bula sun roki a sako su, yayin da suke tsaye a gaban kyamara. “Hakika suna firgice kuma sun damu, amma suna kokarin danne zuciyarsu,” inji rahoton.
“Kowacensu ta dan taka gaba zuwa wajen wani farin kyalle da aka makala a jikin wasu bishioyi. Hudu daga cikinsu za a ji su radau suna fadi cikin harshen Hausa cewa an kama su ne da karfi kuma suna jin yunwa. Wata doguwar yarinya mai kimanin shekara 18 ta fadi a lokacin da take zubar da hawaye tana cewa: “Iyayena suna cike da damuwa.” Wata kuma da ke magana a hankali cewa ta yi: “Ban yi tsammanin zan shiga cikin wahala haka ba a rayuwata.” Ta uku ta ce: “Sun dauke mu da karfi ne.” Yayin da yarinya ta hudu ta yi korafi cewa: “Ba mu samun wadataccen abinci.”
Jaridar ta ruwaito cewa ’yan matan da ke cikin faifan bidiyo suna cikin koshin lafiya, sai dai wasunsu sun kamu da rashin lafiya, ciki har da wadda ta karye a hannu.
Ta ce an dauki bidiyon ne a ranar 19 ga Mayu, kuma an nuna wa Shugaba Jonathan don “tabbatar da suna raye,” tare da karfafa gwiwar Shugaban kasar ya amince da tayin ’yan Boko Haram na musaya da mayakansu.
A ranar Talata fadar Shugaban kasa ta tabbatar da karbar sabon faifan bidiyon da ke nuna ’yan matan Chibok suna rokon Shugaba Jonathan ya taimaka wajen ceto su daga Boko Haram.
Kakakin Shugaban kasa, Dokta Doyin Okupe ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na CNN.
Daga farko jami’an gwamnati sun musanta samuwar wannan faifan bidiyon, sai dai Okupe ya shaida wa CNN cewa ya ga bidiyon da ’yan matan suke rokon a sako su.
Wani faifan bidiyo da Boko Haram ta fitar a ranar 12 ga Mayu, ya nuna kimanin ’yan mata 130 suna zaune a kasa sanye da hijabi suna karanta wasu ayoyin Alkur’ani. Kuma a cikin bidiyon ne aka nuna shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yana tayin musayar ’yan matan da ’ya’yan kungiyar da ke tsare.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta rika nanata cewa ba za ta amince da bukatar ba.
A makon jiya Babban Hafsan Tsaro, Iya Marshal Aled Badeh ya ce, gwamnati ta san inda ’yan matan na Chibok suke, amma ba za a dauki matakin soja don kwato su ba, saboda tsoron salwantar rayuwarsu.
Ya ki yin karin bayani, yana mai cewa hakan zai dada sanya ’yan matan a cikin hadari. Majiyoyi sun ce sanarwar ta Badeh mai yiwuwa ta biyo bayan ganin sabon bidiyon ne, inji Mail on Sunday. Rahoton ya ce an raba ’yan matan a sansani akalla hudu.
Shi dai Dokta Stephen Dabis, wanda mutumin kasar Ostereliya ne da ya ba shugabannin Najeriya uku shawara kan yadda za a sasanta da kungiyoyin masu dauke da makamai a kasar nan, ya shafe watan da ya gabata yana kokarin taimakawa a sako ’yan matan.
Ya ce, “Mafi yawan ’yan matan Chibok din ba a Najeriya ake tsare da su ba. An rarraba su rukuni-rukuni a iyakokin Najeriyya da Kamaru da Chadi da Nijar. Na ce, ‘mafi yawansu ne’ kamar yadda wani karamin rukuni da ke Najeriya ya tabbatar min a makon jiya, a lokacin da muka nemi a sako su.” Kuma ya bayyana yadda tattaunawar ke tafiyar hawainiya.
“daya daga cikin ’yan matan da ke wadancan kananan rukunonin na fama da rashin lafiya kuma muna fatar shawo kan kwamandan rukunin ya sako ta, ta yadda za mu yi jinyarta,” inji Dokta Dabis.
Ya kara da cewa: “Akwai wasu ’yan matan da ba su da koshin lafiya, kuma muna dab da cimma nasarar ganin an sako su, sai dai wadanda suka kama su suna tsoron ko wani tarko ne na kokarin kama su a yayin mika su. daya daga cikin ’yan matan ina jin tana fama da abin da nake tsammanin karaya ce a hannu, kamar yadda suka nuna min yadda take rike hannun nata. Kuma an gaya min akwai wasu da ba su da lafiya da suke bukatar a yi musu magani.”