‘Yan matan Chibok: Sun zame wa gwamnati karfen kafa
A ranar Alhamis din makon jiya ce, aka cika shekaru biyu cif-cif da `yan kungiyar Boko Haram suka yi wa Makarantar `yan mata ta garin Chibok, Hedkwatar karamar Hukumar Chibok ta Jihar Barno dirar mikiya a cikin tsakar dare, suka kuma yi awon gaba da `yan mata 276, da suke zaman rubuta jarrabarsu ta karshen […]
A ranar Alhamis din makon jiya ce, aka cika shekaru biyu cif-cif da `yan kungiyar Boko Haram suka yi wa Makarantar `yan mata ta garin Chibok, Hedkwatar karamar Hukumar Chibok ta Jihar Barno dirar mikiya a cikin tsakar dare, suka kuma yi awon gaba da `yan mata 276, da suke zaman rubuta jarrabarsu ta karshen karatun Sakandaren waccan shekarar. A cikin wancan adadi rahotanni sun tabbatar da cewa wasu `yan mata 57, sun samu kubuta ta hanyoyi daban-daban, walau ko dai a cikin daren ta hanyar yin kasada suka diro daga cikin motar da ke dauke da su, ko kuma ta hanyar gudowa daga dajin da aka kai su bayan fakon idanun `yan kungiyar ta Boko Haram. Tun a wancan lokaci zuwa yanzu ake ta fafutikar ganin yadda za a ceto sauran `yan mata 217, da ke hannun `yan kungiyar Boko Haram.
Duk da yake kafin da bayan kama ko sace `yan matan na Chibok, ’yan kungiyar Boko Haram din sun yi ta sace mutane maza da mata yara da manya a garuruwa daban-daban a shiyyar Arewa maso Yamma, inda nan rikicin tadakayar bayan tasu ta dauko asali, ta kuma fi kamari tun a shekarar 2009, da suka fara ta, amma dai sace `yan matan Sakandaren na Chibok, shi ya fi kowane shiga bakin duniya, ta yadda har ma ta kai faagen da tsohuwar Ministar Ilmi Dokta Obiageli Ezekwesili, ta kasance ta gaba-gaba cikin wadanda suka kirkiro kungiyar neman maido da `yan matan Chibok da ake kira Bringbackourgirls, wato BBOG.
Bayan yekuwa da gangamin da kungiyar ta BBOG ta dukufa akai a nan cikin gida don ceto `yan matan, ta kuma himmatu wajen matsa wa gwamnati lamba don ganin ta inganta hanyoyin sadarwa da matakan tsaron kasar nan, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas. kungiyar ta BBOG, ta kuma nemi gwamnati da lallai sai ta rinka tanadar kariya ta musamman ga kananan yara da suke zuwa makaranta don gudun kar a ci gaba da sace su, ko kame su, ta kuma kare su daga barazanar yin lalata da su, balle azabtar da su ko kuntata musu, tare da tabbatar da ana hukunta duk wanda aka samu da laifin aikata makamancin hakan ga kananan yaran.
Duk da irin kuntatawa da barazanar da `yan kungiyar BBOG din suka rinka fuskanta a cikin gwagwarmayarsu, musamman daga Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, da rana daya `yan kungiyar ba su taba sassautawa ba cikin neman a sako `yan matan har kawo wa yau din nan. Wannan ta sanya ba wai a nan cikin gida kadai aikace-aikacen kungiyar BBOG suka samu karbuwa ba, a`a, hatta a kasashen irin na nahiyar Turai da Amurka da makamantan kungiyoyi, sun ji kururuwar kungiyar sun kuma amsa. Alal misali, uwargidan shugaban kasar Amurka Madam Michelle Obama ita ma ta baza yekuwar a maido `yan matan na Chibok. Su ma Firayiministan kasar Birtaniya mai ci yanzu Mista Dabid Cameron da kuma wanda ya gabace shi, wanda yanzu Jakada na musamman a kan fannin ilmi na Majalisar dinkin Duniya Mista Gordin Brown, duk sun shiga cikin yekuwar yadda za a sako `yan matan na Chibok. Haka shi ma Asusun yara na Majalisar dinkin Duniya, wato UNICEF, ba a bar shi a baya ba.
Ita ma yariyan nan `yar kasar Pakistan mai rajin kare hakkin ilmin `ya`ya mata, Malala Yousafazai,`yar shekaru 17 da haihuwa, ta bi sahun al`ummar duniya da kungiyoyi wajen ganin an sako `yan matan, a lokacin da ta kawo ziyara kasar nan, a tsakiyar watan Yulin shekarar 2014.
Da a ce yadda kungiyar BBOG da kungiyoyin kasa da kasa da Gwamnatin Jihar Borno da iyayen `yan matan Chibok din suka dukufa akan fafutikar ganin an sako `yan matan tun da farko haka Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ta dauki al`amarin, to, kuwa da ba a kawo wannan lokaci ba a na batun an sace `yan matan, ballantana kuma a ce har ya zuwa wannan lokaci ba a samu kwato su ba. Amma sai aka wayi gari Gwamnatin Shugaba Jonathan ta ma rinka nuna shakkunta a kan ma an sace `yan matan, karshe ma dai sai da ta kai Matar Shugaban kasar Dame Pateince, a wani taro da ta yi da iyayen `yan matan da Shugabar Makarantar da Shugaban karamar Hukumar Chibok da sauran masu ruwa da tsaki daga Chibok din, aka ji tana cewa “Yanzu haka `yan matan su suka bi `yan kungiyar ta Boko Haram.” Cikin kuma zare idanu irin na mulkin wancan zamani kalaman da ko kadan ba su yi wa Gwamnatin Jihar Barno da iyayen `yan matan da `yan kungiyar ta BBOG dadi ba. Daga wancan lokaci Gwamnatin Jonathan ta shiritar da maganar.
Duk da yake wasu daga cikin `yan matan Chibok din 57 da suka kubuta, sun samu tallafin ci gaba da karatunsu da sake tsugunnar da su akan wata sabuwar rayuwar a nan cikin gida da waje. Ita kuma gwamnatin tarayya ta jam`iyyar APC ta ci gaba da yin hobbasar ganin an kubuto da wadancan `yan matan. Amma kuma wasu rahotanni na tabbatar da cewa gwamnatin tana cikin rudanin da wane bangare na `yan kungiyar ta Boko Haram za ta yi hulda da su don ceto `yan matan, idan har ma suna nan a raye. Alal misali rahotannin baya-bayannan suna nuni da cewa saboda irin matsin lambar kawo karshen gwagwarmayar `yan kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin tarayya ta dukufa akai, yanzu ana zargin `yan kungiyar Boko Haram din sun kasu gida uku, kowane bangaere yana sanya nashi sharuddan da za a sasanta da shi, sasantawar da aka ce wata kasar Turai na shiga tsakani. Baya ga rahoton da gwamnatin take da shi na cewa, `yan kungiyar Boko Haram din sun karkasa `yan matan zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar nan irin su Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da ma dajin Sambisa da ke cikin kasar nan.
Ana cikin wannan danbarwa ce kuma sai ga tashar Talabijin ta CNN kwanannan ta nuna wasu `yan mata 15, da suka alakanta kansu da su `yan matan Chibok, wadanda daya bayan daya kowace ta ambaci sunanta, sannan wata ta fadi cewa sunanan lafiya, suka kuma gitta wa gwamnatin taayya sharuddan da za a aiwatar har a sako su, an ce a cikin watan Disamban bara aka dauki wannan faifai. A zaman martanin gwamnatin tarayya an ji Ministan Yada labarai Alhaji Lai Mohammed yana cewa, gwamnati tana nazarin faifan bidiyo din da nufin ta iya tantancewa cewa anya kuwa ba shi ba ne wanda aka nuna can baya ba. A fadar ministan gwmnati da iyayen yara a kullum suna cike da fatan ganin an ceto `yan matan, amma kuma tana taka-tsan-tsan akan gaskiya bayanan da suke bijoro mata. Tabbatas yadda ake samun matsin lambar a ceto `yan matan na Chibok, musamman daga manyan shugabanni duniya da kungiyoyin kasashensu, ka iya cewa har ya fi yadda ake son a kawo karshen gwagwarmayar `yan kungiyar ta Boko Haram. Allah Ya kiyaye.