’Yan matan FGC Yauri 11 na hannun ’yan bindiga bayan watanni 10 da sace su
Dogo Gide ya gina gida mai kyau na zamani a wata unguwa a Birnin Gwari.
Nan da kwanaki kadan masu zuwa wasu dalibai mata 11 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi, za su cika watanni 10 da yin garkuwa da su bayan sace su da fitaccen dan bindigar nan da aka fi sani da Dogo Gide ya yi.
A ranar 17 ga watan Yunin shekarar bara ne aka kai wa makarantar ta Birnin Yauri hari inda aka sace dalibai da dama da malamai biyar a makarantar ta kwana wadda mallakar Gwamnatin Tarayya ce.
- Dalibai da ma’aikatan FGC Yauri sun kubuta
- Daliban FGC Yauri 2 sun tsere daga hannun ’yan bindiga
- Sojoji sun ceto daliban FGC Yauri 9 daga hannun masu garkuwa
A halin yanzu dai akwai ragowar ‘yan dalibai mata 11 suna da ke ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindigar duk da biyan kudin fansa da musayar fursunoni da aka yi a lokuta daban-daban.
Aminiya ta ruwaito a ranar 21 ga watan Fabrairu cewa, akalla dalibai mata 13 ne aka aurar da su ga ’yan daban daji inda har wasu daga cikinsu sun samu juna biyu.
Haka kuma, jaridar ta ruwaito cewa an yi garkuwan da daliban akalla makarantu 10 a shekarar bara yayin da ’yan bindiga suka kai hari a wasu makarantu a jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da Kebbi.
Satar mutanen ta biyo bayan harin farko da wasu ’yan bindiga da ke kai hari a yankin Arewa maso Yamma suka kai farmaki a watan Disambar 2020, lokacin da wasu gungun ’yan ta’adda karkashin jagorancin Auwal Daudawa, suka kai hari a makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina inda suka sace dalibai sama da 200.
Yadda aka debe tsammani tsawon lokaci
Harin na Kwalejin FGC Yauri, wanda ya faru ne kasa da kwanaki 20 da sace daliban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina a Jihar Neja, ya haifar da ce-ce-ku-ce a lokacin kan batun tsaron lafiyar daliban, musamman a makarantun da ke kewayen da matsalar tsaro ta shafa.
Nan da nan bayan sace ’yan matan, jami’an tsaro suka kwato kadan daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, yayin da ’yan bindigar suka sake su a wani bangare na tattaunawa da aka cimma yarjejeniya.
Daga baya an sako da dama daga cikin wadanda aka sace a matsayin rukuni na biyu bayan sasantawar da aka yi a watan Oktoba da Janairu.
Gide, wanda ake kyautata zaton shi ne dan bindigar da ya fi kusanci da Kungiyoyin Jihadi, saboda doguwar alakarsa da kungiyar Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Bilad as-Sudan wadda aka fi sani da Ansaru, a wata tattaunawa ta wayar tarho ya yi barazanar sauya daliban ta hanyar horar da maza akan amfani da bindiga tare da aurar da matan.
Kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram, ta sha yi wa wadanda ta sace ikirarin irin wannan horarwar, musamman ‘yan matan Chibok da aka sace tun a shekarar 2014.
Wasu da ke da masaniya kan kokarin ganin an sako wadanda lamarin ya rutsa da su sun shaida wa Aminiya cewa, Jagoran ’yan bindigar ya cika alkawarinsa yayin da ya aurar da akalla 13 daga cikin daliban.
An ce an bayar da ’yan matan ne ga ’yan bindigar da ’yan Kungiyar ISWAP masu da’awar jihadi a Yammacin Afirka, a cewar iyayen daya daga cikin ’yan matan da ba su so a bayyana sunansu ba.
Ana kyautata zaton ISWAP da Ansaru suna da sansani a cikin dazukan Birnin Gwari da yankunan da suka hada da jihohin Kaduna da Neja da Zamfara.
An kuma ce wasu daga cikin ’yan matan na auren wasu masu sha’awarsu da ke zaune a kauyukan da ke iyaka da yankunan da Dogo Gide ke jagoranta a wajen garin Birnin Gwari.
Jagoran ’yan bindigar na rike da daliban ne duk da cewa, ya karbi makudan kudade a matsayin kudin fansa tare da sakin mutanensa biyu a wani bangare na tattaunawa a watan Oktoba, kamar yadda Aminiya ta ruwaito a lokacin.
Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi Shawara na Musamman Kan Harkokin Tsaro, Garba Rabi’u Kamba, bai amsa kiran wayar tarho domin jin ta bakinsa kan wannan labari ba, amma a watan Fabrairu ya shaida wa Aminiya cewa, akwai dalibai 14 da ’yan bindigar suka sako.
Sai dai wata tattaunawar sasanci tsakanin iyaye da masu garkuwa da mutane ta ce, an sako uku daga cikin ’yan matan makarantar ga iyayensu a tsakiyar watan Janairu, wanda ya rage adadin zuwa 12.
An ce ’yan matan uku sun dawo ne da juna biyu.
Amma Aminiya ta gano cewa, bayan da aka sake sakin wata yarinya guda daya mai suna Ummi a cewar wata majiya mai tushe a ranar Litinin da ta gabata, a yanzu ’yan mata 11 suna tare da wannan jagoran ’yan bindigar.
Wakilinmu ya tattaro rahoton cewa, Gide ya dage kan sasantawa da gwamnati, ya bukaci a biya Naira miliyan 100 don fansar ’yan matan. Sai dai babu wani ci gaba a wannan bangaren. “Tare da gwamnati na yin watsi da sauye-sauyen shawarwarin, Gide yakan sa iyaye su yi shawarwarin da daidaikun mutane,” a cewar wata majiya da ta saba ba da rahoton sasantawar.
Wata mahaifiyar daya daga cikin ’yan matan da ta kamu da rashin lafiya bayan ta gano ‘yarta ba ta cikin rukunin karshe na daliban da masu garkuwa da mutanen suka sako a watan Janairu, ta ce a tsakiyar watan Maris an tuntubi masu garkuwa da su, inda suka bukaci su biya kudin fansar diyarsu kan Naira miliyan 10.
Wani dan uwan wadanda aka sace ya shaida wa Aminiya cewa, mahaifiyar yarinyar ta tattauna da wadanda suka yi garkuwa da su kuma sun amince da Naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa, inda aka aika ta hannun wani mai shiga tsakani a Birnin Gwari ta hanyar tura kudin ga masu sana’ar POS a garin.
“An fitar da kudin ne aka kai musu a inda suke kusa da Kamfanin Doka. Sun karbi kudin, amma sun ki sakin yarinyar,” inji majiyar.
A cikin wani faifan murya da Aminiya ta samu, an ji dan bindigar da ya tattauna kuma ya karbi kudin fansar yana musanta cewa, yana da halin kubutar da yarinyar, ko da tun da farko ya yi alkawarin zai gana da Gide don a sake ta.
Ya yi ikirarin cewa, an yi kuskuren sunansa da na Gide, ya gargadin mai kiran da ya daina kiransa sannan kuma ya daina amsa kiran mahaifiyar dalibar.
’Yan bindiga na rayuwa cikin ‘yanci
Kamar sauran Kungiyoyi masu dauke da makamai da ke da sansanoni a dazukan da suka ratsa jihohin Kaduna da Neja da Zamfara, an ce Gide da mutanensa suna zaune cikin walwala a Unguwar Birnin Gwari na Kamfanin Doka da yankin Gwaska.
“Gide ya gina gida mai kyau na zamani a Unguwar da yake zaune kuma kwanan nan ya gayyaci mahaifiyarsa wurin.
“Ya gabatar da mahaifiyar ga ’yan matan kuma ta yi mu’amala sosai da su, ciki har da tattaunawa da wasu iyayensu ta wayar tarho,” inji wani da ke magana da daya daga cikin ’yan matan da ake tsare da su.
Ya ce, yayin da ’yan matan tun farko an hana su tattaunawa da ’yan uwansu, kwanan nan ne aka bude layukan sadarwa tsakanin wadanda aka sace da iyayensu.
“’Yata na yin magana da mahaifiyarta akai-akai amma yawancin lokuta ana sa ido yayin da ’yan bindigar ba sa taba bari su yi magana da su ba tare sanin abin da suke tattaunawa don guje wa sanin bayanan sirri.”