’Yan Najeriya 400 ke gudun hijira a kan iyakar Kamaru

Kimanin ’yan gudun hijira mutum 400 daga kasar Afirka ta Tsakiya ke  neman agajin gaggawa,  bayan da suka samu kansu a cikin wani mawuyacin hali a iyakokin kasar kamaru da Jamhoriyar Afrika ta tsakiya (CAR).Wata majiya ta bayyana wa Aminya ta wayar tarho cewa ’yan Najeriya sama da 400 na gudun hijirar ne sakamakon rikicin […]

’Yan Najeriya 400 ke gudun hijira a kan iyakar Kamaru
’Yan Najeriya 400 ke gudun hijira a kan iyakar Kamaru

Kimanin ’yan gudun hijira mutum 400 daga kasar Afirka ta Tsakiya ke  neman agajin gaggawa,  bayan da suka samu kansu a cikin wani mawuyacin hali a iyakokin kasar kamaru da Jamhoriyar Afrika ta tsakiya (CAR).
Wata majiya ta bayyana wa Aminya ta wayar tarho cewa ’yan Najeriya sama da 400 na gudun hijirar ne sakamakon rikicin da ya  barke tsakanin Kristoci da Musulmai a kasar Afrika ta tsakiya (CAR), inda ’yan tsirarun Musulmin kasar ke gudun hijirar sakamakon hare-haren da kristocin suke kai musu.
Wani  suna Muhammadu Mustafa da ke cikin ’yan gudun hijirar a garin Kentjou, da ke karamar Hukumar Bature cikin Jihar Defua a kasar kamaru, ya sheda wa ’yan jarida ta waya cewa  suna cikin mawuyacin hali a kan iyaka.
Ya ce, daukacin ’yan gudun hijirar sun fi dubu 10, amma wadanda suka tabbatar ’yan Najeriya ne, su 400, inda ya tabbatar da cewa, sun fi wata daya a kan iyaka, amma ba wata gudumuwar da suka samu daga hukumomin Najeriya ko na Kamaru.
Ya kara da cewa, sun yi kokarin ganawa da Jakadan Najeriya a Kamaru, amma al’amarin ya ci tura. Domin ba su da takardar izinin shiga kasar. Har yanzu dai suna nan a iyakar Kamaru, kuma suna cikin mummunan hali da neman agaji.
Mustafa ya bayyana cewa, ba su da abinci, babu gurin kwana kuma babu mai tallafa musu. “idan mun kamu da rashin lafiya, ba a karbar mu a asibiti har sai sun ga mutum ya kusa mutuwa, inji shi.
Ya ce, har yanzu shiru dai suke ji babu alamun agaji ko taimako.