’Yan Najeriya 40m na fama da cutar barci —Gwamnati

Ministan Kimiyya da Fasaha ya ce mazauna karakara miliyan 40 na fama da cutar barci a Najeriya.

’Yan Najeriya 40m na fama da cutar barci —Gwamnati

Ministan Kimiyya da Fasaha Dakta Onu

Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu ya bayyana cewa akalla mutum miliyan 40 ne ke fama da cutar barci a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da ofishin ma’aikatar shiyyar Arewa maso Gabas a Jihar Gombe a karshen makon da ya gabata.

Ya ce cutar da kudan tsando ke haddasawa na kama mutane da dabbobi, kuma hakan babbar asara ce ga tattalin arziki.

Ya kara da cewa cutar da aka fi sani da cutar talakan karkara, ta fi shafar manoma, masunta, masu yawon bude ido da makiyaya.

Akalla shanu miliyan 19.5, tumaki miliyan 22 da awaki miliyan 34 ne ke fuskantar barazanar harbuwa da cutar.

Dakta Onu ya kara da cewa kudaden da ake kashewa wajen samar da magungunan cutar na da yawa.

Ya kara da cewa Jihar Gombe za ta samu fa’idoji da yawa sakamakon bude ofishin hukumar a jihar.

Ya kara da cewa an zabi jihar Gombe ne saboda ficen da ta yi wajen kiwon shanu.

Sannan ya ce sabon ofishin zai taimaka wa manoma da zarar an fara ba da tallafin wuraren kiwon shanu a kasar nan.